‘Yan Bindiga Sun Shiga Fada, Sun Yi Garkuwa da Basarake, An Bindige Wata Har Barzahu
- A daren Talata aka samu wasu miyagu dauke da bindigogi, sun sace Sarkin Oghara a jihar Kogi
- Ana zargin ‘yan bindigan sun yi garkuwa da Basaraken ne domin su samu kudin fansa a kansa
- Harin ya yi sanadiyyar wata mai aiki a fadar Sarkin, sannan an hada da wasu Dattawa an dauke
Kogi - Mai rike da sarautar kasar Oghara a karamar hukumar Kabba Bunu ta jihar Kogi, yana hannun ‘yan bindiga a yanzu da ake tattara rahoton nan.
Wani labari mara dadi da ya fara fitowa a Daily Trust, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun je fadar Basaraken a tsakar daren Talata, suka yi gaba da shi.
A wajen wannan mugun hari, an rasa wata daga cikin ma’aikatan Sarkin. An tabbatar da mutuwar Toyin Onare wanda miyagun suka budawa wuta.
Rahoton ya ce baya ga Mai martaban da aka yi nasarar daukewa, ‘yan bindigan sun tsere da wasu Dattawa biyu; Pa David Obadofin da Cif Temidayo Elewa.
'Yan sanda sun fitar da jawabi
Kakakin ‘yan sanda na reshen Kogi, SP William Aya ya tabbatar da haka ga manema labarai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
William Aya yake cewa da kimanin karfe 3:00 na dare wadannan miyagu suka shigo fadar Basaraken, su ka shiga harbe-harbe ko ta ina, kafin suyi ta’adin.
Jawabin ‘yan sanda ya ce Kwamishinan jihar Kogi, CP Hakeem Yusuf ya tada runduna ta musamman ta karade yankin domin ceto wadanda aka dauke.
An ji bayan harba bindigogi a sararin samaniya, sai aka shigo fadar, aka dauke Basaraken.
An hada da su David Obadofin
Tsautsayi ya aukawa David Obadofin wanda yana cikin manyan manoma kuma daya daga cikin Sarakunan yankin Oghara a lokacin da yake cikin gidansa.
Wata jaridar ta ce Cif Obadofin yana tare da wani yaronsa a lokacin da aka kawo harin, aka hada da shi da Temidayo Elewa, aka shiga jeji da su a daren.
Wani daga cikin wadanda aka dauke ya tsere a lokacin da ake hanya, babu labarin sauran.
Ita kuwa Toyin Onare da aka harba, sai da aka isa babban asibitin gwamnati na garin Kabba, sannan aka tabbatar da cewa bindigar tayi sanadiyyar ajalinta.
NBC: Shari’ar tarar N5m
Rahoton da mu ka fitar a baya, ya bayyana cewa wasu sun yi karar Mai girma Shugaban Najeriya a Kotu a dalilin tarar kudin da aka ci tashar Channels.
Kalaman Yusuf Datti Baba Ahmed a kan Bola Tinubu su ka jawo NBC ta ci Channels TV tarar N5m, SERAP da CJID sun shigar da kara, sun ce an saba doka.
Asali: Legit.ng