Duk Duniya Babu Mahalukin da Zai Dakatar da Rantsar da Tinubu, Inji Gwamnan APC Umahi

Duk Duniya Babu Mahalukin da Zai Dakatar da Rantsar da Tinubu, Inji Gwamnan APC Umahi

  • Gwamnan jihar Ebonyi ya bayyana matsayarsa game da rantsar da Bola Ahmad Tinubu a ranar 229 ga watan Mayu mai zuwa
  • Zababben gwamnan jihar, Francis ya gabatar da takardar lashe zaben gwamna da hukumar zabe ta INEC ta bashi a kwanan nan
  • Gwamna Umahi ya sake jaddada aniyarsa ta zama shugaban majalisar dattawa, ya fadi mafarkinsa game da kujerar

Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya yi martani ga masu son kawo tsaiko ga rantsar da Bola Ahmad Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A cewar Umahi, duk duniyar nan babu wanda ya isa ya dakatar da sabon shugaban kasan na Najeriya wata mai zuwa, Aminiya ta ruwaito.

Umahi ya fadi wadannan kalaman ne a lokacin da zababben gwamnan jihar, Francis Nwifuru ya ziyarce shi a ranar Talata 11 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Jagaba Ba Za Ka Shiga Villa Ba: Kotu Ta Hana Belin Mai Zanga-Zangar Kin Jinin Rantsar Da Tinubu

Babu mai hana rantsar da Tinubu, inji Umahi
Zababben shugaban kasa Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya shaida cewa, a zaben na bana, Bola Ahmad Tinubu ya tsallake matsaloli da yawa kafin Allah ya bashi nasarar lashe zaben.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sabon gwamnan ya gabatar da takardar shaidan lashe zabe

A ziyarar da Francis ya kai wa gwamnan, ya gabatar masa da takardar shaidan lashe zaben gwamnan jihar da hukumar zabe ta INEC ta ba shi.

Da Umahi ke jawabi:

“A lokacin da na ce muku Tinubu zai ci zabe, ba ku yarda da batu na ba. Bari na sake jaddada muku, duk duniyar nan babu mahalukin da zai iya hana rantsar da shi a watan gobe.
“Dalili kuwa shi ne, lokacin da za a iya dakatar da shi, sai Allah ya ce shi ne. Tun da kuwa Allah ya zabe shi, babu wanda ya isa ya ce ba haka ba.”

Kara karanta wannan

"PDP Ba Za Ta Kai Labari Ba Idan Har Ta Ba Dino Melaye Tikitinta a Zaben Gwamnan Kogi", Wike

Umahi ya lashe kujerar sanata

A zaben da ya gabata, an sanar da gwamna Umahi a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan mazabarsa na ranar 25 ga watan Faburairu.

Hakazalika, gwamnan na zawarcin kujerar shugaban majalisar dattawa da ake ci gaba da cece-kuce a kanta a kasar, rahoton Vanguard.

A cewar Umahi, ya sha yin mafarkin zama shugaban majalisar dattawa, inda a yanzu yake son gaje kujerar Ahmad Lawal.

Peter Obi ya shirga karya game da zaben 2023

A wani labarin, hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa na Labour ya shirga game da zaben da aka kammala.

A cewar INEC, ya kamata kotun zabe ta yi watsi da karar da Peter Obi ya shigar da ke kalubalantar sakamakon zaben.

Ta bayyana cewa, ‘yan Najeriya sun fito gaba dayansu ne don ba Tinubu kuri’unsu sabanin ikrarin na Peter Obi wai shi yaci zabe.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin Arewa 6 da na Kudu 2 da ka iya zama ministoci a mulkin Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.