Allah Ya Yiwa Mbadinuju, Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Rasuwa a Birnin Tarayya Abuja
- Allah ya yiwa daya daga cikin tsoffin gwamnonin Najeriya rasu bayan gajeriyar jinya a babban birnin tarayya Abuja
- An ruwaito cewa, Dr Chinwoke Mbadinuju ya rasu yana da shekaru 78, kamar yadda dansa ya sanar a wata sanarwa
- Dan nasa ya bayyana halin da aka shiga, ya kuma bayyana irin jimamin da ake ciki a halin yanzu
FCT, Abuja - Rahoto ya bayyana sanar da rasuwar tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr Chinwoke Mbadinuju.
An ce Mbadinuju ya rasu ne a babban asibitin tarayya da ke Abuja ranar Talata 11 ga watan Afrilu, yana da shekaru 78 a duniya, Punch ta ruwaito.
Mbadinuju, wanda aka fi sani da "Odera", ya kasance gwamnan Anambra a tsakanin 1999 zuwa 2003 a karkashin jam'iyyar PDP.
Dansa ne ya tabbatar da mutuwarsa
Wata sanarwar da dansa Mista Cheta Mbadinuju ya sanyawa hannu a madadin iyalansa ya kuma rabawa manema labarai a ranar Talata, ta bayyana cewa ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Da kuncin zuciya amma muna matukar godiya ga Allah bisa yadda ya yi rayuwa mai kyau, muna sanar da rasuwar mahaifinmu, kakanmu, kawunmu, abokinmu kuma amininmu Dokta Chinwoke Mbadinuju, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dattijon kasa.
“Odera, kamar yadda ake kiransa, ya rasu yana da shekara 78 a duniya da safiyar ranar 11 ga Afrilu, 2023 a asibitin kasa da ke Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya, sadda yake zagaye da iyalansa da masoyansa.
“A wannan lokacin kunci, muna addu’ar Allah ya jikansa da rahamarsa ya ba wadanda ya bari hakurin rashi. Ahalinsa za su sanar da shirye-shiryen jana'izarsa nan ba da jimawa ba."
An ce Mbadinuju ya mulki jihar Anambra ne a daidai lokacin da jihar ta fuskanci rudanin siyasa, rahoton Daily Trust.
Fasto ya mutu garin kwaikwayar Annabi Isa
A wani labarin kuma, kunji yadda wani fasto dan kasar Mozambique ya kwanta dama a garin kwaikwayon Annabi Isa.
An ruwaito cewa, mutumin ya kuduri yin azumi ne na kwanaki 40 domin kusantar ubangiji, amma rai ya yi halinsa.
An bayyana yadda yunwa ta galabaitar dashi, har ya zama ba zai iya motsi ko yin wani abun a zo a gani ba.
Asali: Legit.ng