Karya Peter Obi Ya Shirga, ’Yan Najeriya Ne Suka Zabi Tinubu, Inji INEC Ga Kotun Zabe
- Hukumar zabe ta INEC ta nemi a watsar da karar da karar da Peter Obi ya shigar game da sakamakon zaben shugaban kasa
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Obi ke ci gaba da ririta cewa, ba Tinubu ne ya lashe zaben bana ba, shi ne ya ci
- A baya kunji cewa, Atiku Abubakar na PDP ne ya zo na biyu a zaben 25 ga watan Faburairu, Peter Obi kuma na uku
FCT, Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bukaci kotun kararrakin zabe ta PEPC da ta yi watsi da karar da jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi suka shigar, inda ta ce batutuwan da suka gabatar basu da tushe.
INEC ta bayyana hakan ne a martanin da ta gabatar a ranar Litinin a sakatariyar PEPC ta hannun lauyanta, Abubakar Mahmoud (SAN) a Abuja, Tribune Online ta ruwaito.
Hukumar ta roki kotun da ta kora ko kuma ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta, kalaman cin zarafi, rashin fahimta, shubuha da rashin daidaito da ke cikinta.
Yadda Peter Obi ya shigar da kara a gaban kotu
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Obi da jam'iyyarsa ta Labour sun kai karar hukumar zabe INEC, Sanata Bola Tinubu, Sanata Kashim Shettima da jam’iyyar APC ne a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 4 bi da bi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi da Labour na neman a soke sakamakon zaben da ya samar da Tinubu da Shettima a matsayin wadanda suka lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Martani irin wannan jam'iyyar APC ta yi game da karar da Peter Obi ya shigar a gaban kotun, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Tinubu wanda ya lallasa ‘yan takara 17 da suka yi takara zaben, ya samu kuri’u 8,794,726, wanda shi ne ya samu mafi yawan kuri'u cikin 'yan takarar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya zo na biyu a zaben da kuri’u 6,984,520 sai kuma Obi da ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.
Fani-Kayode ya nemi a kamo Atiku da Peter Obi
A wani labarin, kunji yadda jigon APC ya yi kira ga hukumomi su kama 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar da Peter Obi.
Femi Fani-Kayode ya fadi hakan ne a martani ga ikrarin hukumar DSS na cewa, akwai masu kitsa hanyar kafa gwamnatin wucin gadi a kasar nan.
Ya bayyana cewa, alamomi sun nuna akwai hannun 'yan takarar na jam'iyyun adawa don ganin ba a rantsar da Bola Ahmad Tinubu ba.
Asali: Legit.ng