Ramadan: Wani Mutumi Ya Daɓa Wa Lamami Wuka Ana Tsaka da Sallar Asuba

Ramadan: Wani Mutumi Ya Daɓa Wa Lamami Wuka Ana Tsaka da Sallar Asuba

  • Liman na cikin Sallar Asuba a wani Masallaci, wani mutumi ya lallaɓo ya daba masa wuka har sau biyu
  • Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya shammaci mutane ya shiga har gurin liman lokacin da aka yi Sujjada
  • Mutane sun yi namijin kokari suka kama maharin kuma suka miƙa wa 'yan sanda don ɗaukar mataki

USA - Wani mutumi da ba'a san manufarsa ba ya shiga cikin Masallaci ana cikin sallar Asubaa, ya soka wa limamin da ke jan Sallar wuƙa a New Jersey da ke ƙasar Amurka.

Aminiya ta rahoto cewa mutumin ya soka wa Lamamin mai suna, Imam Sayed Elnakib, wuƙa da sanyin safiyar ranar Lahadi da ta gabata cikin wata mai Alfarma.

Masallata a Masallaci.
Ramadan: Wani Mutumi Ya Daɓa Wa Lamami Wuka Ana Tsaka da Sallar Asuba Hoto: aminiya
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa wannan abu ya faru ne a Masallacin Omar kuma ya raunata Liman ɗan kimanin shekara 65 a duniya.

Kara karanta wannan

Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android, Ya Kone Kurmus

Sai dai a halin yanzun rahotannin da suka fito daga Asibitin da aka kai Imam Sayed sun nuna yana murmure wa a hankali a hankali daga raunin da ya samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin an kama wanda ya caka wa limamin wuƙa?

Bugu da ƙari, bayan aikata wannan ɗanyen aiki, Masallatan da ke bin Limamin sun yi namijin kokarin damƙe mutumin wanda aka gano sunansa, Serif Zorba, ɗan shekara 32 a duniya.

Na'urorin ɗaukar hoto na tsaro sun fallasa yadda mutumin ya shammaci mutane lokacin da suka tafi sujjada, ya kutsa har zuwa wurin liman ya daɓa masa wuƙa.

Mutumin ya yi kokarin guduwa bayan aikata wannan ɗanyen aiki amma Musulmai suka bi shi da gudu suka damƙe shi har sai da yan sanda suka ƙariso.

Wani da abun ya faru a gabansa ya faɗa wa kafar watsa labarai ta CBS cewa:

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

"Nan take Limamin ya ce wayyo ya yi ajalina ku gaggauta kama shi, ya zubda jini sosai sakamakon raunin da aka ji masa a wuya."

Mai magana da yawun Masallacin ya ce sau biyu aka daba wa Liman wuƙa duk da akwai Masallata kusan 200 a lokacin.

Buhari Zai Bar Najeriya Fiye da Yadda Ya Same Ta, Adesina

A wani labarin kuma Fadar shugaban kasa ta faɗi namijin kokarin da Buhari ya yi a yaƙi da matsalar tsaron Najeriya

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina, ya ce idan aka kwatanta kafin zuwan Buhari, da bayan ya karɓi mulki, banbancin a bayyane yake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262