Hotunan Yadda Mai Mata 2 Ke Cin Duniyarsa da Tsinke Tare da Matansa Sun Jawo Cece-Kuce

Hotunan Yadda Mai Mata 2 Ke Cin Duniyarsa da Tsinke Tare da Matansa Sun Jawo Cece-Kuce

  • Jama’a sun yi ta cece-kuce bayan ganin wani kalan daukar hoto na wasu ma’aurata; mata biyu da mijinsu daya
  • An ga masoyan na cin duniyarsu da tsike a cikin kaya iri daya, ga kuma mijin na kwance a kan cinyoyin matansa biyu
  • Kishin wasu mata ya tashi a kafar sada zumunta, wasu kuma suka ce ba za su taba iya auren namijin da ke da mata ba

Wasu hotuna sun yadu a kafar sada zumunta na yadda wani magidanci yake shan soyayya daga matansa kyawawa, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Mutumin da ba a gano waye shi ya sanya kaya iri daya da matansa biyu, inda suka dauki hotuna masu daukar hankali.

A daya daga cikin hotunan da aka yada a TikTok, mutumin ya kwanta a kan cinyoyin matansa biyu kamar karamin yaro. A sauran hotunan kuwa, yana sumbatarsu a baki.

Kara karanta wannan

An samu tangarda: Saurayi ya fusata, ya kone gidan su tsohuwar budurwarsa kurmus

Yadda mai mata biyu ke cin duniyarsa da tsinke
Hotunan mai mata biyu da matansa | Hoto: @lakpadesire0
Asali: TikTok

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kafar sada zumunta ta dauki dumi, mutane sama da miliyan 4 ne suka kalli hotunan da ke cike da cece-kuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli hotunan:

Martanin jama’a

Mutane da yawa sun bayyana abin da suka ji da ganin wadannan hotunan masu daukar hankali, ga kadan daga ciki:

@Call-mi-Diva:

“Babu wanda naga yana magana game da hoto na ukun.”

@Queen daro:

“Wannan ba zai taba faruwa dani ba, ba kuma zai faru da tsatso na ba.”

@user37352094517020:

“Allah ya mana rahama mu mata.”

@osehtarawally2:

“Ka yi abin da ke saka maka farin ciki, wannan shine kyawun rayuwa.”

@Fafa Jocelyne:

“Ba zan taba hada miji da wata ba gaskiya ‘yan uwa mata Musulmai ina taya ku murna.”

@Ismael Coulibaly290:

“Dan uwana har yanzu saura maka biyu ka cike abin da Allah ya shar’anta maka.”

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

@Omarion:

“Na duba martanin jama’a, kamar wasu basu taba ganin haka ba, amma iyayenku 2 da 2 ne a gida, daidai ne.”

Yadda saurayi ya gwangwaje budurwarsa da abinci mai ban mamaki

A wani labarin kuma, kun ji yadda wani saurayi ya ba budurwarsa abinci mai daukar hankali a lokacin da ta kai masa ziyara.

An ga hoton doya da manjan da saurayin ya ba budurwar, lamarin da ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter.

Mutane da yawa sun bayyana cewa, ba laifi bane don ya ba ta kalan abincin, watakila iyakar abin da yake dashi kenan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.