An Kama Yan Sanda Da Ke Ba Wa Rarara Tsaro, Za Su Gamu Da Fushin Hukuma
- Rundunar yan sandan Najeriya ta cafke jami'an ta da ke ba wa Dauda Kahutu Rarara, fitaccen mawaki mazaunin Kano kariya bayan fitowar wani bidiyo
- Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook ya yi tir da abin da aka ga yan sandan na yi a wani bidiyo
- An ga yan sandan na biya da Rarara ne har ya shiga mota kuma suka rika harbi sama don kambana shi, amma Rararan ya musanta hakan ya ce suna kokarin korar bata-gari ne
Rundunar yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu jami'anta da ke ba wa fitaccen mawakin siyasar nan mazaukin Kano, Dauda Kahutu Rarara kariya.
Wani bidiyo da ya yadu a dandalin sada zumunta ya nuna yan sanda da ke ba wa Rarara kariya suna biye da shi a baya lokacin da ya shiga mota har suka harba bindiga a sama.
Muyiwa Adejobi, kakakin rundunar yan sanda cikin wata sako da ya fitar ta shafinsa na Facebook ya ce:
"Rundunar ta yi Allah-wadai da rashin kwarewa da halin rashin da'a da yan sandan suka yi na harba bindiga don kuranta mawakin na Kano."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya cigaba da cewa:
"An binciko yan sandan an kuma kama su. Za a tafi da su hedikwatar yan sanda don musu tambayoyi tare da daukan matakin da ya dace a kansu."
Hakazalika, ya ce irin halayan da suka nuna ba ta jami'an yan sanda bane kuma ba za a amince da hakan ba, rahoton TRT Afirka.
Martanin Rarara kan harbin da yan sandan suka yi
Cikin wani hira da aka yi da mawakin a bidiyo, ya ce ba domin kuranta shi yan sandan masu tsaronsa suka yi harbin ba.
A cewar Rarara:
"Mun tafi rabon abinci ne a Kahutu, sai wasu ɓata-gari suka so tada tarzoma, a nan wurin ne muka samu matsala yan sandanmu suka yi harbi sama."
Ya kara da cewa yan sandan ba su yi amfani da hayaki mai saka hawaye ba domin ana azumin ramadana.
Rarara ya soki gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a wata sabuwar waka da ya fitar
A wani rahoton daban kun ji cewa Dauda Kahutu Rarara wanda ya shahara wurin yi wa Shugaba Buhari da yan APC waka ya cacaki Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.
Daily Trust ta rahoto cewa an gano mawakin ba ya goyon bayan Dr Nasiru Yusuf Gawuna, dan takarar gwamnan APC na jihar Kano a zaben 2023.
Asali: Legit.ng