Najeriya Ta Biya Bashin Tiriliyoyin Kudaden da Taci Daga Waje, Ta Sake Runtumo Bashi

Najeriya Ta Biya Bashin Tiriliyoyin Kudaden da Taci Daga Waje, Ta Sake Runtumo Bashi

  • Gwamntin Najeriya ta yi nasarar biyan bashin N3.63trn da bankin duniya da sauran wadanda suka ba kasar rance ke binta
  • Wadanda suka ba Najeriya rance sun karbi wadannan kudaden ne tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2022 da a gabata
  • Duk da cewa biyan bashin labari ne dai madadi, amma gwamnati ta sake runtumo wasu tiriliyoyin kudin da suka kusan ninka wanda ta biya

A cewar rahoton ofishin kula da bashi (DMO) da Legit.ng ta samo, Najeriya ya kashe N3.63trn wajen biyan bashin waje da na cikin gida a shekarar 2022 da ta gabata.

Wadanda suka samu nasarar samun biyan bashin sun hada da gwamnatin China, bankin Muslunci, bankin Larabawa, hukumar ba da lamuni ta duniya da dai sauransu.

Gwamnatin Najeriya ta biya bashin da ake binta
Buhari ya rage bashin da ake bin Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yadda Najeriya ta biya wani adadin kudin da ake binta bashi

Kara karanta wannan

An samu tangarda: Saurayi ya fusata, ya kone gidan su tsohuwar budurwarsa kurmus

Duba ga alkaluman hukumar DMO, Najeriya ta yi amfani da farashin 448.08 wajen biyan bashin dala 2.40bn, wanda ya yi daidai da N1.07trn.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bangare guda, ta biya bashin cikin gida da ya kai N2.56trn, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Kudaden cikin gida da Najeriya ta biya sun hada da masu zuba hannun jari, bankuna da dai sauran wadanda aka ci kudadensu.

DMO ya bayyana cewa, adadin kudaden da aka kashe wajen biyan bashi a watan Afrilun 2022 bai haura 529.88bn ba.

Adadin kudaden da aka biya a kowane wata a rancen cikin gida

A kasa mun tattaro muku jerin kudaden da aka biya a kowane wata daga asusun gwamnati a 2022.

  1. Janairu - N188.36bn
  2. Faburairu - N103.88bn
  3. Maris - N376.44bn
  4. Afrilu - N529.88bn
  5. Mayu - N66.97bn
  6. Yuni - N67.88bn
  7. Yuli - N248.72bn
  8. Agusta - N152.44bn
  9. Satumba - N419.42bn
  10. Oktoba - N302.42bn
  11. Nuwamba - N57.24bn
  12. Disamba - N47.11bn

Kara karanta wannan

Biyu Babu: Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta

Rancen kasashen waje da Najeriya ta biya

  1. China - $256,583,866.48
  2. International Monetary Fund – $14,908,327.22
  3. African Development Bank - $114,170,633.49
  4. International Fund For Agricultural Development - $6,364,700.31
  5. African Development Fund - $29,287,792.35
  6. Africa Growing Together Fund - $389,139.37
  7. International Development Association - $446,064,137.09
  8. European Development Fund - $5,243,339.76
  9. Arab Bank for Economic Development in Africa - $632,181.86
  10. Islamic Development Bank - $1,552,989.77
  11. India - $8,166,901.40
  12. France - $46,825,104.25
  13. Germany - $24,978,907.67

A baya dama rahoto ya bayyana adadin kasahsne da ke bin Najeriya bashi mai yawan gaske a shekarar 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.