Babbar Magana Yayin da APC Ta Dakatar da Sanata Daga Jihar Gombe Saboda Zargin Cin Amanar Jam’iyya
- Labarin da muke samu daga jihar Gombe na bayyana yadda aka dakatar da wani sanata a jam’iyyar APC
- Wannan ya faru ne sakamakon zarginsa da cin dunduniyar jam’iyyar a zabukan da suka gabata a kasar nan
- Ba wannan ne karon farko da aka dakatar da wani mai rike da kujerar siyasa ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa
Balanga, jihar Gombe - Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu a majalisar dattawa, Bulus Amos ya gamu da fushin jam’iyyar APC mai mulki.
An ruwaito cewa, jam’iyyar a matakin gundumawar Bambam ta karamar hukumar Balanga ta dakatar da sanatan daga ci gaba da zama mamban APC, Punch ta ruwaito.
Shugaban APC na gundumar, Muhammad Kaka ne ya bayyana dakatarwar, inda ya zargi sanatan da cin dunduniyar jam’iyyar a zaben da ya gudana.
A cewarsa, an kafa kwamitin mutum biyar da za su titsiye sanatan don gano ayyukansa na cin dunduniyar jam’iyyar mai mulkin kasa da jihar Gombe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amos ya yi kokari, bai ci amanar APC ba, inji wani hadiminsa
Sai dai, wani mai ba shi shawari, Amos Manessa Felix ya musanta zargin da ake yiwa sanatan, inda yace ya yi kokari wajen nasarar APC a zaben da ya gudana.
A cewar Felix, mai gidan nasa ya yi aiki tukuru wajen ganin APC ta samu nasara a matakin shiyya da ma jihar ta Gombe, rahoton TheCable.
Da yake tabbatar da dakatar da sanatan a wani taron manema labarai, sakataren yada labarai na APC Moses Kyari ya ce dakatarwar na zuwa ne bayan da ‘yan gundumarsa suka shigar da bukatar hakan.
Sanata ya gaza kare kansa a gaban kwamitin APC
Ya kara da cewa, hakan ya sa APC ta kafa kwamitin mutum biyar domin tabbatar da gaskiyar zargin da ake masa ko akasin haka nan da makwanni biyu.
A cewar Kyari, a lokacin daka gayyaci sanatan, ya gaza wanke kansa daga zarge-zargen da ake masa a gaban kwamitin.
APC ta kori ministan Buhari
A wani labarin, kun ji yadda jam’iyyar APC ta yi ragin nauyi a jihar Enugu, inda ta dakatar da mutane da yawa.
Wannan ya faru ne sakamakon zarginsu da cin dunduniyar jam’iyyar a zaben shugaban kasa da na gwamnan da ya gabata.
Daga cikin wadanda aka dakatar, har da ministan Buhari da kuma tsohon gwamna da wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Asali: Legit.ng