Ortom Ya Yi Ta'aziyyar Kashe Mutane 134, Ya Roki Buhari Ya Turo Sojoji
- Gwamnan jihar Benuwai ya koka kan yawaitar kashe-kashen rayuka yan kwanakin nan a wasu yankuna
- Ya roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya cika kalamansa a aikace ta hanyar kara girke sojoji
- A dazu, shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin da ka kai sansanin yan gudun hijira a jihar Benuwai
Benue - Gwamna Sanuel Ortom na jihar Benuwai, ya buƙaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya tabbatar da kalamansa a aikace kan kashe-kashen kwanan nan a jihar.
A cikin mako ɗaya da ya gabata, yan bindiga da ake zargin muggan makiyaya ne sun kashe mutane 134 a kananan hukumomin Otukpo, Guma, da Apa a jihar Benuwai.
Channels tv ta ce gwamna Ortom ya yi wannan rokon ne yayin da ya kai ziyara ƙauyen Mgbam, gundumar Nyiev, ƙaramar hukumar Guma, inda aka kashe mutane 36 ciki harda yan gudun hijira.
A wani harin na ranar Litinin, aƙalla mutane 47 suka rasa rayukansu a ƙauyen Ikobi, karamar hukumar Apa, ciki har da Dagaci. Bayan haka aka kashe mutum 51 ranar Laraba a Umogidi, yankin Otukpo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Biyo bayan rasa rayuka 134 jumulla kenan a kwana 5, gwamna Ortom ya nuna takaicinsa kan yadda sansanin yan gudun hijira da kauyuka suka zama wurin da 'yan ta'adda suka matsa wa lamba.
Lokacin da ya kai ziyara ƙauyen Mgbam, Ortom ya koka kan yadda kashe-kashe suka yawaita, ya nemi agaji daga shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
A halin yanzun waɗanda suka jikkata a hare-haren baya-bayan nan na kwance a Asibitin koyarwa na jami'ar jihar da ke Makurdi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Buhari ya yi tir da hare-haren
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Asabar, Buhari ya yi tir da ƙaruwar rikice-rikicen da kashe-kashen mazauna jihar Benuwai cikin mako ɗaya.
Ya umarci jami'an DSS, rundunar 'yan sanda, rundunar soji da sauran hukumomi su ƙara kaimi kuma su sake nazari kan yanayin tsaron yankunan da lamarin ya taɓa.
A wani labarin kuma Gwamna El-Rufai Ya Cire Dokar Kullen Da Ya Ƙaƙaba a Wani Yankin Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta ɗage dokar zaman gida ta awanni 12 da ta sanya a yankin ƙaramar hukumar Chikun.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce Sojoji da yan sanda zasu ci gaba da sintiri don tabbatar da bin doka da oda.
Asali: Legit.ng