Rayyuka Sun Salwanta Yayin Da Motocci Suka Yi Karo A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Rayyuka Sun Salwanta Yayin Da Motocci Suka Yi Karo A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

  • Bayin Allah guda uku sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummun hadarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar 8 ga watan Afrilu kamar yadda wani Saidu Ibrahim da abin ya faru gabansa ya fada
  • Daga bisani jami'an Hukumar Kiyayye Haddura na Kasa, FRSC, sun iso wurin domin tallafawa wadanda abin ya shafa, an mika gawar wadanda suka rasu ga iyalensu

Jihar Kaduna - A kalla mutane uku sun riga mu gidan gaskiya sannan wasu sun jikkata yayin da motocci biyu suka yi karo a babban hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wani wani abin ya faru a gabansa, Saidu Ibrahim, ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Mararaban Ida, a safiyar ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Bauchi Ta Ɗage Zaman Muƙabala Da Sheikh Dr Idris Abdulaziz

Hatsari
Rayyuka Sun Salwanta Yayin Da Motocci Suka Yi Karo A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce hatsarin ya hada da wata Toyota Highlander mai rajista KWL 198 KA da Volkwagen golf mai lamba MKA 89 ZY.

Ibrahim ya ce direban Highlander din ya taho da gudu daga yankin Kaduna ya kuma sha gaban wata mota ya yi karo da mota kirar Golf da ta fito daga Abuja.

Ya ce:

"Direban golf din ya fito ne daga yankin Abuja motarsa cike da lemu da wasu 'ya'yan itatuwa yana hanyarsa ta zuwa kauyen Gidan Abe, yayin da Highlander Jeep din ta taho da gudu daga wurin da aka raba hanya ta yi karo da golf din."

Wakilin majiyar Legit.ng Hausa wanda ya isa wurin jim kadan bayan hatsarin, ya ce ya hangi gawar mutum biyu daga motar golf din an kwantar da su a gefen titi.

Kara karanta wannan

Biyu Babu: Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta

Jami'an Hukumar FRSC sun kawo dauki

An kuma ga wasu jami'an hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, suna kokarin cireo wani da ya makale a cikin mota.

Mutanen bakwai da suka jikkata an garzaya da su zuwa Babban Asibitin Sabon Wuse.

An mika gawarwakin wadanda suka rasu ga iyalensu

Wani jami'in hukumar FRSC cikin wadanda suka yi aikin ceton, ya ce an mika gawarwakin mutanen uku da suka rasu ga iyalansu bayan sun nuna hujjar cewa yan uwansu ne.

Mutane 18 sun kone kurmus sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da su a Bauchi

A wani rahoton a baya, kun ji cewa wasu mutane 18 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su.

The Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 4.40 na yammacin ranar Laraba a jihar ta Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164