Mutum 18 Sun Kone Kurmu a Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

Mutum 18 Sun Kone Kurmu a Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

Bauchi - Mummunan lamari ya faru a jihar Bauchi da yammacin Laraba yayin da aka samu mugun hatsari da ya lashe rayukan mutum 18 inda suka kone har ba a iya gane su a wurin kauyen Nabardo kan babban titin Bauchi zuwa Jos, jaridar The Punch ta rahoto.

Lamarin an gano ya faru ne wurin karfe 4:40 na yammacin ranar Laraba a jihar Bauchi.

Mummunan hatsarin ya hada ne da motocin haya gida biyu, mota kirar Toyota Hiace Bas da tirelar MAN.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel