An Rufe Karatun Alƙur'ani da Tafseeri a Fadar Shugaban Kasa Kan Abu 1
- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya samu halartar rufe tafsirin Alƙur'ani mai girma a Masallacin gidan gwamnati
- Wannan shi ne karo na karshe da za'a gudanar da karatun da Buhari a matsayin shugaban ƙasa
- An rufe karatun ranar Jumu'a ne sakamakon Limamin Masallacin zai tafi Umrah kasa mai tsarki
Abuja - Shugaban kasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya bi sahun 'yan uwa Musulmi wajen halartar rufe Tafseerin Alƙur'ani mai girma a masallacin gidan gwamnati da ke Abuja.
Premium Times ta rahoto cewa an rufe Tafsirin bana 2023 da wuri-wuri ne saboda limamin Masallacin fadar shugaban ƙasa zai tafi kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah.
Karanta ayoyin littafi mai tsarki da kuma bayanin ma'anoninsa watau 'Tafseer' na gudana a Masallacin a kowace rana tsawon watan Azumin Ramadan, wata na 9 a jerin watannin Musulunci.
Sai dai Tafsirin bana na shekarar 2023 yana da muhimmanci na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari domin shi ne na karshe da zai gani a matsayin shugaban Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa ya ce:
"Yayin da shugaban kasa ke dab da kammala zangon mulkinsa na biyu nan da 'yan makonni, Limamin Masallacin, Sheikh Abdulwahab Sulaiman, ya maida Tafsirin na bankwana."
A wurin rufe karatun Alƙur'anin na bana, Sheikh Sulaiman, ya yaba wa shugaban kasa Buhari bisa hakurinsa da juriya tsawon lokacin mulkinsa.
Haka zalika ya ƙara yaba wa Buhari bisa matakin da ya ɗauka na yaƙar cin hanci da rashawa, ta'addanci da rashin tsaro, da kuma kokarin da ya yi wajen ayyukan raya ƙasa.
Bugu da ƙari, Limamin Masallacin ya jinjina wa shugaba Buhari bisa kafa kyakkyawan tsarin sauke nauyi da kuma yi wa ƙasa hidima da al'ummar cikinta cikin gaskiya da rikon amana.
Daga nan kuma aka gudanar da Addu'ar samun nasara ga gwamnati mai zuwa ƙarƙashin shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
An sanar da kuɗin kujerar Hajji a Najeriya
A wani labarin kuma Hukumar NAHCON Ta Sanar da Kuɗin Kujerar Hajjin Bana, Ta Raba Su Zuwa Kaso 8
Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da kuɗin kujerar aikin Hajjin 2023, inda adadin kuɗin kujerar ya rabu zuwa kashi 8.
Shugaban hukumar ya ce kuɗin na farawa daga miliyan N2.8m, amma ya danganta da jihar da maniyyaci ya fito.
Asali: Legit.ng