Gwamnati Ta Gama Shirin Janye Tallafin Fetur, An Karbo $800m Daga Bankin Duniya
- Bankin Duniya ya ba Gwamnatin Najeriya $800m da za ayi amfani da su bayan cire tallafin fetur
- Ministar tattali, tsare-tsare da kasafin kudi ta ce za ayi amfani da kudin wajen taimakawa talakawa
- Baya ga yayyafin da za ayi wa marasa galihu, Zainab Ahmed ta nuna za su tanadi motocin hawa
Abuja - Gwamnatin Najeriya tayi nasarar karbo $800m a hannun Bankin Duniya yayin da ake ta kokarin cire tallafin da ke kan man fetur a kasar.
Jaridar Leadership ta ce Ministar tattali, tsare-tsare da kasafin kudi, Zainab Ahmed ta shaidawa manema labarai wannan bayan zaman FEC a Abuja.
A karshen taron majalisar zartarwa da Muhammadu Buhari ya jagoranta, Zainab ta ce an karbo kudin da za ayi amfani da su a taimaki marasa karfi.
Ministar ta ce za a raba bangaren wannan kudi ne talakawa kimanin miliyan 50 da ke cikin ha’ula’i.
A jawabin da tayi a fadar Aso Villa, an fahimci cewa gwamnatin tarayya ba ta ware wasu kudi domin biyan tallafin man fetur daga Mayun 2023 ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Zainab Ahmed
"A yayin da mu ke aiki a kan shirin kasafin kudi da MTEF na shekarar 2023, mun cire tanadin da ake yi wa kasafin kudi daga watan Yuni.
Mu na kan aiki, mu na tattaunawa da masu ruwa da tsaki dabam-dabam, bayan haka mun samo wasu kudi daga hannun bankin Duniya.
Wannan ne kason farko na kudin da za mu samu damar rabawa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a al’umma da mu ke da su a rajistarmu.
A yau rajistar na kunshe da gidaje miliyan goma. Gidaje miliyan goma daidai yake da mutum miliyan 50.
- Zainab Ahmed
Wasu matakan da za a dauka
Premium Times ta rahoto Ministar kudin ta na cewa za a nemi karin kudi domin yin wasu ayyukan da za su rage radadin karin farashin man fetur a kasar.
Rahoton ya ce daga cikin hanyoyin da za a bi shi ne a kawo motocin da ‘yan kwadago za su rika hawa, game da kudin da za a raba kuwa, har shiri ya yi nisa.
Lokacin kammala ayyuka
An rahoto Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yana cewa ranar 30 ga watan Afrilu ne sabon wa’adin kammala babban titin Legas zuwa Ibadan.
Baya ga haka, an ji dalilin da Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta sauka, ba a gama gina hanyar Abuja-Kano ba da Ministan ya je duba wani aiki da aka karasa.
Asali: Legit.ng