Tashin Hankali Yayin Da Yan Bindiga Suka Raba Malamin Addini Da Ransa A Jihar Arewa
- Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun katse wa wani fasto a jihar Kogi hanzari yayin wani hari da suka kai cocinsa
- Maharan sun afka cocin ne yayin da ake addu'ar safe a cocin Living Faith da ke unguwar Aloko-Oganenigwu a karamar hukumar Dekina
- Wani mamban cocin mai suna Samuel ya ce faston da farko ya tsere amma ya yanke shawarar ya dawo ya duba mabiyansa shine lamarin ya ritsa da shi
Jihar Kogi - Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun yi ajalin wani faston cocin Living Faith Church, Aloko-Oganenigwu a karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi, Jacob Wodi Hulobu, wanda suka mamaye garin ranar Lahadi.
Daily Trust ta rahoto cewa faston ya tsere da mutanensa zuwa wani wurin da suke ganin ya fi tsaro amma yan bindigan suka kai musu hari da safe yayin da suka addu'a.

Kara karanta wannan
An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

Source: Facebook
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar daya cikin mambobin cocin mai suna Samuel, faston ya koma ya duba halin da mambobinsa ke ciki bayan harin, sai yan bindigan suka harbe shi.
Samuel ya ce:
"Ya tsere yayin addu'ar safe a cocin. Ya yi tsammanin komai ya lafa kuma ya koma ya duba idan an taba cocinsa a lokacin ne aka halaka shi."
City & Crime ta gano cewa faston, wanda da farko ya wallafa yadda ya tsira daga harin farkon a shafinsa na Facebook da safe, ya ce ga garinku bayan yan awanni.
An ce Hulobu ta shirya taron ne na kirista da aka yi wa lakabi da 'Let the fire fall: Three nights of Wanders,' da za a yi daga ranar 13 ga watan Afrilu zuwa 15 a cocin kafin afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan
Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha
Faston ya rabu ya bar matarsa da da guda daya.
An Kama Yan Kungiyar Ta'addanci Da Ke Addabar Nasarawa Da Abuja
A wani rahoton kun ji cewa yan sandan Abuja sun yi nasarar kama mambobin wata mugunyar kungiya da ake zarginsu da adabar mutanen jihar Nasarawa da Abuja.
Sadiq Abubakar, kwamishinan yan sandan Abuja ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a wani otel da ke unguwar Masaka a jihar Nasarawa da ke kusa da Abuja, rahoton The Cable.
Asali: Legit.ng