“Baki Kyauta Ba”: Jama’a Sun Caccaki Budurwar da Ta Fusata Saboda Saurayinta Ya Ba Ta Doya da Manja

“Baki Kyauta Ba”: Jama’a Sun Caccaki Budurwar da Ta Fusata Saboda Saurayinta Ya Ba Ta Doya da Manja

  • Wata budurwa ta kada kafar sada zumunta bayan da ta yada abincin da aka ba ta lokacin da ta ziyarci wani saurayinta
  • Budurwar ta ziyarci saurayin nata ne a karon farko zuwa gidansa, inda ya yanke shawarin dafa mata abincin da za ta ci
  • Sai dai, abin da zai iya ba ta ba komai bane face tafasasshen doya da manya da kuma ruwan leda gama-gari

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna @nihiinn a Twitter ta yanke shawarin zurfafa alakarta da wani saurayinta, ta ziyarce shi har gida.

Don burge ta, matashin ya zauna, inda ya hada mata abinci mai dadi dafin gida da ba zai yi wahalan samu ba.

Nan take ya dafa doya, ya baje ta da manja kana ya dauko ledar ruwa ya danka ma budurwar. Lokacin da ya ba ta abincin, sai kawai ta fusata.

Kara karanta wannan

"Ko Ba Shi Da Hannu Zan Zauna Da Shi": Labarin Zazzafar Son Da Jaruma Rakiya Moussa Ke Yi Wa Wani Mawaki Ya Girgiza Intanet

Yadda budurwa ta fusata bayan saurayi ya bata doya da manja
Kalan abincin da saurayi ya ba budurwarsa | Hoto: @nihiinn
Asali: Twitter

Cikin fushi ta dauki hoto abincin, kana ta yada shi a kafar Twitter don bayyana yadda ta ji game da wannan saurayin nata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

“Na ziyarci wannan mutumin a karon farko. Ya bani doya da manja da ledar ruwa.”

Sai dai, jama’ar kafar sada zumunta sun caccake ta bisa daukar hoton abincin da saurayin ya bata tare da yada shi a Twitter.

Martanin jama’a

Ga kadan daga abinda jama’a ke cewa bayan ganin rubutun budurwar:

@dominnos:

"Daukar hoton abincin da kuma dauka shi a intanet babban rashin mutunci ne. Ya za ki yi idan ya gani?”

@cherry25634:

"Karya ne. Mamarki ce ta ba ki wannan.”

@oyin_gucci:

"Kina da gishiri zan kara ne a cikin manjan?”

@iam_jhessica:

"Ban ga wani munin abu ba da yin hakan. Sai dai idan baki jituwa da doya da manja.”

Kara karanta wannan

Jirgin Najeriya: Bidiyon yadda wata mata ta shide a jirgi, ta gaza numfashi saboda cunkoso

@evablazin23:

"Na jima ban ci wannan ba. Bari na tafi na siyo doya, ina da manja.”

@killertunes_tii:

"Wannan shine soyayyar gaskiya (sashen talauci).”

@nnenna_blinks_:

"Zan ci sannan na sumbace shi a goshi. Wannan na daya daga cikin abincin da nake so. Akalla dai ya cika cikinki. Watakila abin da yake dashi da zai iya baki kenan.”

@nancy_phil:

"Ce masa zan yi mu daga albasa da danyen tattase mu saka akai.... zai fi dadi.”

@comradejerrbernard:

"Ba dai kinci ba ko, ina dai kin ci?”

@bolaadenike:

"Laifinsa daya kawai watakila ruwan bai da sanyi saboda matukar ruwa babu sanyi, doya ba za ta wuce ba sai da ruwan sanyi.”

@eriggapaperboi:

"Doyan da nake ci ba zai bani wani tsoro ba.”

Wata budurwa ta ce ba za ta iya auren mai albashin N70,000 a wata, jama'a sun yi martani mai daukar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.