Ganin Hoton Tinubu a Kasar Faransa Ya Girgiza Intanet, Jama’a Sun Yi Martani Mai Zafi
- Sabon hoton da aka yada na Bola Ahmad Tinubu ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter a jiya Litinin
- An ga lokacin da Tinubu ke tare da matarsa a cikin wani hoto, inda aka ce an dauke shi ne a lokacin suna da kasar Faransa
- Jama’ar kafar sada zumunta, musamman ‘yan adawa sun bayyana rashin amincewa, sun nemi ganin bidiyon zababben shugaban kasan
Kafar Twitter - Zababben shugaban kasan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana a kasar Faransa, inda aka ga yana cin duniyarsa da tsinke gabanin rantsar dashi.
An gano Tinubu ne tare da matarsa Oluremi a kasar ta Faransa a cikin wani hoton da ofishinsa na yada labarai ya saki a ranar Litinin da dare.
Duk da cewa ‘yan a mutun Peter Obi; Obidients basu ji dadi da ganin hoton ba, kana sun yi cece-kuce akai, an ce suna tsammanin ganinsa sharkaf a gado, amma lafiyarsa lau.
Hoton mai daukar hankali ya jawo cece-kuce a kafar Twitter, inda magoya bayan Tinubu ke masa fatan alheri da ci gaba tare da matarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Martanin jama’a a kafar sada zumunta
Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani kan wannan hoton, wasu na suka, wasu kuma na yabo da fatan alheri. Ga kadan daga ciki mun tattaro muku:
@markdondish:
“Yana shiri gabanin sanya kunzugunsa ko.”
@tega_okonedo:
“Ku nuna mana sabbin hotunan shugabanmu da aka kaka mana.”
@Abim4S:
“Madalla hotunan shugaban kasa mai jiran gado da uwar gidansa.”
@Kings_CEO:
“Don tabbatar mana da sabon hoto ne, ya kamata Tinubu ya yi bidiyo kuma yana magana game da halon da Najeriya ke ciki. Idan ba haka ba, wata karyar ce kawai daga shaidanun APC.”
@ShinkafiAbbakar
“Mai girma shugaban kasa da uwar gidansa kenan.”
Ba Tinubu bane zabin Allah, cewar Peter Obi na LP
A wani labarin, kunji yadda dan takarar jam’iyyar adawa ta LP, Peter Obi ya bayyana matsayarsa game da sakamakon zaben shugaban kasa na Najeriya.
Peter Obi ya ce sam ba Allah ne ya zaba ma ‘yan Najeriya Tinubu ba, don haka a daina ta’allaka rashin gaskiya ga siyasar kasar nan.
A tun farko, Obi ya ce sam ba zai amince sakamakon zaben nan ba tun bayan da aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe.
Asali: Legit.ng