Bayan Sace Ɗalibai Mata 2, An Jibge Jami'an Tsaro a Jami'ar Tarayya Gusau

Bayan Sace Ɗalibai Mata 2, An Jibge Jami'an Tsaro a Jami'ar Tarayya Gusau

  • An kara jibge jami'an tsaro a gidajen da ɗaliban jami'ar tarayya Gusau ke haya a garin Sabon Gida, jihar Zamfara
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu 'yan fashin daji sun shiga sun yi awon gaba da ɗalibai mata guda 2
  • Har yanzun shugabannin jami'ar ba su ce komai ba game da lamarin amma kakakin 'yan sanda yace sun fara kokarin ceto su

Zamfara - An ƙara tura karin jami'an tsaro zuwa yankin gidajen da ɗalibai ke zama a kauyen Sabon Gida bayan ɗalibai mata biyu sun shiga hannun masu garkuwa ranar Lahadi.

Wasu da ake zaton 'yan fashin daji ne sun yi awon gaba ɗaliban jami'ar tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara mata guda biyu bayan sun kutsa cikin gidajen da suke haya a Sabon Gida.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kewaye Gari Guda, Sun Kashe Rayukan Mutane Sama da 40 a Watan Azumi

Daliban da aka sace a jami'ar Gusau.
Bayan Sace Ɗalibai Mata 2, An Jibge Jami'an Tsaro a Jami'ar Tarayya Gusau Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa daga zuwan maharan suka ɗauee masu gadi kuma suka ƙwace wayoyinsu, daga bisani suka sace ɗaliban mata biyu da ke karantar Kwas ɗin microbiology.

Sabon Gida ne garin da jami'ar tarayya Gudau take kuma bai wuce kilomita ɗaya ba tsakaninsa da ainihin cikin jami'a. Ɗalibai sun saba amsar hayar gidaje a garin su zauna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan abinda ya faru, ɗaliban sun tsorata sun bar gidajen amma daga baya suka koma bayan mahukunta sun kara jibge ƙarin jami'an tsaro domin ba su kariya.

Har yanzun mahukuntan jami'ar ba su ce komai ba game da abinda ya faru, duk wani ƙoƙarin tuntubar jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar domin jin ta bakinsa ya ci tura.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce tuni suna kaddamar da Operation ɗin ceto ɗaliban da aka sace.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Miji da Mata da Ɗiyarsu Sun Rasu Suna Tsaka da Bacci a Kaduna

Yace tawagar dabaru da sanin aiki na yan sanda sun bazama bincike da nufin ceto ɗalibai matan guda biyu daga hannun yan ta'adda, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wani ɗalibin jami'ar FUGUSAU ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa sace ɗaliban ya ta da hankalinsu sosai duk da su ɗakunansu na cikiɓ harabar makaranta.

"Ɗauke matan akwai tashin hankali, babu wani nisa takaaninmu, watarana cikin jami'a zasu shigo duk na ga yanzu gwamnati ta tura jami'an tsaro, sojoji su yi gadin wurin," inji shi.

Game da ko maharan sun nemi fansa, ɗalibin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce bai ji labarin tattaunawar da ake da masu garkuwan ba har yanzu.

An Harbe Dalibin Ajin Karshe a Jami'ar UNIBEN Har Lahira a Hostel

A wani labarin kuma Wasu Maharan sun bindige ɗalibin jami'a dake shekarar Karshe, ya mutu nan take a ɗakin kwanan ɗalibai

Kara karanta wannan

Karin Bayani: A Watan Azumi, 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba a Arewa

Lamarin wanda ya faru da daren ranar Litinin, ya jefa tsoro da fargaba a zuƙatan sauran dalibai, sun fara ƙauracewa ɗakunan kwanansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel