Shehin Malamin Musulunci Ya Koka Kan Yawaitar Mace-Mace Aure a Al'ummar Musulmi
- Wani shehin malami a birnin tarayya Abuja ya hango matsala a tsakanin matasan musulmai
- Sheikh Ayuba Abubakar ya hango yadda mace-macen aure ke ƙara yawaita a tsakanin al'ummar musulmai musamman matasa sabon aure
- Shehin malamin ya kawo hanyoyin da yakamata abi domin shawo kan wannan gagarumar matsalar
Abuja- Sheikh Ayuba Abubakar na kotun majistare ta birnin tarayya Abuja, ya nuna damuwar sa kan yadda ake yawaitar mutuwar aure a tsakanin matasa ke ƙaruwa a birnin tarayya Abuja.
Da yake gabatar da jawabi a wajen lakcar shekara-shekara da Afemai Islamic Movement in Abuja ta shirya ranar Lahadi, malamin ya koka kan cewa iyaye basu kiyayewa da dokokin Al-Qur'ani mai girma wajen bayar da auren ƴaƴan su. Rahoton Punch
"A matsayin da nake da shi na alƙali, muna samun yawaitar saki, musamman a birnin tarayya Abuja. Abin tashin hankali. Matasan da basu daɗe da aure suna kai ƙarar raba aure kotu."
”Sannan mun fahimci cewa a mafi yawa daga ciki, babu wata hanyar da ta wuce a raba su kawai kowa yayi ta kansa."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Matsalar hakan shine idan bamu koma bin tafarkin addinin musuluncin muna yi. addu'o'i ba domin samun shiriya daga Allah, za a cigaba da samun irin waɗannan matsalolin."
”Wannan koyarwar ta miji ce ya san haƙƙin sa akan matar sa sannan mata tasan haƙƙin ta da nauyin ta akan mijinta. Waɗannan dokokin zasu kawo zaman lafiya a gidajenmu."
Abubakar ya ƙara da cewa duk da saki abin ƙi ne, an halasta shi a addinin musulunci. Rahoton Daily Trust
"A matsayin ka na musulmi, dole ka tabbatar cewa gidan ka ana bin koyarwar musulunci, gidan da ake karanta Al-Qur'ani a cikin sa, sannan kuna ware lokaci wajen koyawa ƴaƴan ku koyarwae addinin musulunci."
”Ku koya musu hadisan Manzon Allah (SAW) ba wai kawai ku bar su suyi karatun boko ba kaɗai, amma a haɗa da na addinin musulunci ta yadda zasu taso a matsayin masu jin tsoron Allah."
Wata Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta garzaya gaban kotu neman ta datse igiyar auren dake tsakanin ta da mijinta.
Matar auren tace mijin nata yana barazana ga lafiyar ta.
Asali: Legit.ng