Canja Fasalin Kuɗi: Don Allah Ku Rungumi Tsarin eNaira - CBN

Canja Fasalin Kuɗi: Don Allah Ku Rungumi Tsarin eNaira - CBN

  • CBN ya samar da eNaira domin yin amfani dashi wajen saye da sayarwa a manhajar waya
  • Ƴan Najeriya da yawa har yanzu basu maida hankali wajen shiga tsarin ba
  • Babban Bankin Najeriya ya fuskanci haka, yanzu yana kira da Arungumi tsarin

Babban Bankin Najeriya CBN ya roƙi ƴan Najeriya dasu amshi tsarin eNaira.

Yace ƴan Najeriya suyi amfani da kuma su rungumi manhajar yanar gizo gizo a amatsayin wata hanya ta cigaban tsarin amfani da kuɗi ba dole sai na zahiri ba.

Babban Bankin yace, manufar yin haka ya zama dole saboda yanzu haka a duniya abinda ake yayi kenan, Najeriya ma baza'a barta a baya ba.

CBN Bank
Canja Fasalin Kuɗi: Don Allah Ku Rungumi Tsarin eNaira - CBN
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani babban direkta a CBN mai suna Abdulmumin Isa ne ya zayyana haka, a wajen wani taro da ake gudanarwa na baja-koli a juma'ar nan a garin Enugu.

Kara karanta wannan

Ana Saura Wata 2 Cikar Wa'adin Mulkin Sa, Wani Babban Ministan Buhari Yayi Murabus

Yace kasar Najeriya bazata yarda a barta a baya ba a wannan tsarin, saboda haka dole ne ayi mai yiwuwa wajen ganin an dama da ita a wannan tsarin.

Ta bakin wakilin sa, mataimakin direkta, Mr Imoh Esu, yace, tsarin na eNaira da aka soma a octoba 2021, yana da matuƙar muhimmanci - Rahoton Gazettengr.

A cewar sa anyi tsarin ne domin ya bunƙasa musayar kuɗi ta manhaja, wanda zai bada damar sauƙaƙa mu'amala ta ƙudi cikin gaggawa tsakanin gwamnatoci da kuma al'umma kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa.

"Bugu da ƙari, CBN ta haɗa gwiwa da sauran bankunan Najeriya domin samar da katin bai ɗaya. Irin sa na farko a Afirka".

Ya ƙarkare da cewa:

"Wannan tsarin bawai zai rage kuɗin gudanarwa bane , a'a zai rage kuɗaɗen da ake kashewa ne wajen mallakar katin ƙasashen waje. Inji shi.

Jerin abubuwa biyar da CBN ya kuskure yayin gabatar da Sababbin Takardun Naira

Sauya fasalin kudin yazo ya tafi yabar baya da ƙura. Jaridar Legit.ng ta zayyano wani rahoto mai nuni da yadda CBN ga kuskure wasu abubuwa guda 5 yayin gabatar da takardun sababbin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel