Kotu Ta Daure Wani Matashi Na Tsawon Watanni 3 Bisa Kama Shi da Laifin Satar Injin Nika

Kotu Ta Daure Wani Matashi Na Tsawon Watanni 3 Bisa Kama Shi da Laifin Satar Injin Nika

  • An gurfanar da wani matashi bisa zarginsa da sace injin nika a wani yankin jihar Ogun da ke Kudancin kasar nan
  • An tasa keyar matashin zuwa magarkama, inda aka ba shi zabin biyan belin N5,000 tare da ba da kudin injin nikan
  • Dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana abin da doka ta tanada na aikata irin wannan laifi na sata

Jihar Ogun - Wani kotun majistare na Ota a jihar Ogun ya tasa keyar matashi mai shekaru 23, Opeyemi Ademola zuwa magarkama a ranar Litinin bisa laifin satar injin nika na N70,000.

Rahoto ya bayyana cewa, Ademola zai shafe watanni uku ne a gidan gyaran hali bisa aikata laifin sata, Vanguard ta ruwaito.

‘Yan sanda ne suka kamo Ademola tare da gurfanar dashi a kotun bisa zarginsa da yin mummunar dabi’ar ta sata.

Kara karanta wannan

Hirar Waya Da Aka Bankado: Babban Faston Najeriya Bishop Oyedepo Magantu Kan Tattaunawarsa Da Obi

An yankewa matashi hukuncin zaman gidan yari na watanni uku bayan kama shi laifin satar injin nika
Jihar Ogun da ke Kudu maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A hukuncin da ta yanke, Mrs A.O Adeyemi ta ce, Ademola zai tafi magarkama na watanni uku ko kuma ya biya N5,000 a matsayin beli tun da ya amsa laifinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya faru

Hakazalika, ta umarce shi da ya nemo N70,000 ya ba wanda ya yiwa satar a matsayin mayar da darajar injin nikan, The Nigerian Voice ta tattaro.

A tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta E.O Adaraloye ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Maris a wani gida da ke lamba 43 Ojuelegba, yankin Arinko, Ota.

Ya kuma ce, wanda ake zargin ya sace injin nikan ne a gidan wata mata Hajiya Bashirat Adebuyi bayan daukar hankalinta da siyan tuwon rogo na N300.

A cewar jami’in dan sandan, laifin da Ademola ya aikata ya yi daidai da tanadin sashe na 390(9) na kundin manyan laifuka na jihar Ogun, 2006.

Kara karanta wannan

Jaruma Mai Kayan Mata: Sai An Biya N1m Ake Gani Na Ido-Da-Ido, Magana Ta Waya Kuma N250,000

An yanke wa wani barawon janareto daurin watanni 3 a gidan yari

A wani labarin, Timothy David, wani matashi mai shekaru 25 bisa laifin satar janaretan wani mutumin da ya kawo kararsa gaban kotu.

An yanke masa hukuncin ne bayan da ya amsa laifinsa na hada baki da wasu tare da yin satar kayan da ba nasa ba.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Chido Leo ya shaidawa mai shari’a yadda lamarin ya faru da kuma yadda matashin ya shiga gidan wani Kingsley ya saci janareta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.