Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Yi Sauye-Sauye a Majalisarsa, Ya Yi Sabbin Nade-Nade
- Masarautar Kano ta yi sabbin nade-nade tare da sauyawa wasu mukamai a wannan karon, ta fadi dalilin yin hakan a yanzu
- Wannan na zuwa ne bayan kammala zaben gwamnoni a Najeriya, inda jihar ta samu sabon gwamna dan jam’iyyar NNPP
- A bangare guda, kun ji yadda ‘yan siyasar Kano suka fara musayar yawu tun bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar
Jihar Kano - Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi garanbawul ga majalisarsa, inda ya daga darajar wasu daga cikin manyan na kusa dashi da suka nuna kwazo wajen yin aikinsu.
Hakazalika, ya yi sabbin nade-nade a masarautar domin yiwa al'ummar Kano aiki yadda ya dace kamar yadda aka saba.
Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwar da sakataren masarautar, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya fitar, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Zaben Kogi: Jerin jiga-jigan siyasan APC 3 da ke son maye gurbin Yahaya Bello da tasirinsu

Source: UGC
Wadanda aka sauyawa mukamai
Daga cikin wadanda aka kara wa matsayi a masarautar akwai Alhaji Ahmad Ado Bayero daga sarkin gida zuwa Dan Iyan Kano, sai kuma Turkakin Kano, Alhaji Lamido Sanusi Bayero zuwa mukamin sarkin gida.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, an ba Tafidan Kano, Alhaji Mahmud Ado Bayero mukamin Turakin Kano sai kuma Dan Galadiman Kano, Alhaji Haruna Rasheed Sanusi da ya zama Tafidan Kano.
Har ila yau, Alhaji Kabiru Tijjani Hashim, Dan Isan Kano ne ya zama sabon Dan Galadima a masarautar mai dimbin tarihi, Punch ta ruwaito.
Sauran sun hada da Dan Lawan Kano, Alhaji Bashir Ado Bayero da ya zama sabon Lawan Kano da kuma Alhaji Yahaya Inuwa Abbas Dan Majen Kano da ya zama Dan Lawan Kano.
Sabbin mukamai
A bangaren sabbin nade-nade, an yiwa Alhaji Ahmad Kabiru Bayero matsayin sabon Barde Kerarriya da kuma Alhaji Abdulkadir Mahmud a matsayin sabon Magajin Rafin Kano.
Da yake magana bayan wadannan nada-naden, sarkin Kano Bayero ya ce, an ba da mukaman ne bisa la’akari da kwazo da bajintar da suka nuna.
Ya kuma bukace su da su kasance masu wakiltar masarautar Kano da suna mai kyau a duk inda suka tsinci kansu kuma su yi aikinsu don ci gaban masarauta.
A baya, kunji yadda Abba Kabir Yusuf, sabon gwamnan Kano ya shawarci duk wadanda ke gini a filayen gwamnati da su gaggauta dakatar da ginin.
Asali: Legit.ng
