APC Za Ta Maka INEC da NNPP Kotu Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kano

APC Za Ta Maka INEC da NNPP Kotu Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kano

  • Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce za ta dauki mataki game da sakamakon zaben gwamnan jihar da ke Arewa maso Yamma
  • APC ta ce lauyoyinta su fara tattara hanyoyin da za su shiga kotu don tabbatar da kalubalantar INEC da NNPP
  • Kwankwaso ya ce ba zai tsoma baki a harkokin mulkin Abba Gida-Gida ba, ya fadi dalilinsa na fadin haka a siyasarsa

Jihar Kano - Jam’iyyar APC ta umarci lauyoyinta da su kalubalanci dan takarar gwamnan NNPP a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan ayyana shi a matsayin zababben gwamnan jihar Kano na zaben 18 ga watan Maris.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin jam’iyyar, Ahmed Aruwa a ranar Asabar 1 Afirilu, 2023, jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, ayyana zababben gwamnan ya saba da tanadin dokar zabe kamar yadda ya so a dokar Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki a Gaban NNPP a Kano, APC Za Ta Karbe Nasarar Abba a Zaben Gwamnan 2023

APC za ta tafi kotu kan batun sakamakon zabe
Jihar Kano da ke Arewa maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

INEC ta saba doka, inji APC

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ayyana wanda ya ci zaben da INEC ta yi ya saba da tanadin dokar da aka rubuta game da zabe.
“Jam’iyyar APC a Kano na kalubalantar INEC, wacce ta ayyana dan takarar gwamnan NNPP a matsayin wanda ya lashe zabe.
“Abin da INEC ta yi ya saba tanadin dokar zabe ta hanyar ayyana Abba Gida-Gida kamar yadda ya shahara da zababben gwamnan jihar Kano.”

Gawuna ya taya Gida-Gida murnar lashe zabe

Saboda haka ne jam’iyyar a Kano ta umarci lauyoyinta da su gaggauta kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu, rahoton Channels Tv.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Nasiru Gawuna, dan takarar gwamnan APC ya bayyana yiwa Abba Gida-Gida murnar lashe zaben.

Siyasar jihar Kano dai a bana ta zo da sauyi, tsohon gwamna Kwankwaso ya kafa gwamnati ta hanyar karfafa gwiwar Abba Gida-Gida ya zama gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

Ba zan shiga lamarin Abba Gida-Gida ba, inji Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji yadda Rabiu Kwankwaso ya ce ba zai tsoma baki a lamarin da ya shafi tafiyar da mulkin zababben gwamnan Kano ba.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da wasu ke kokarin bayyana cewa, akwai yiwuwar yake tsoma baki a harkokin mulkin jihar.

Kwankwaso ya yi bayani, ya kuma bayyana gaskiyar abin da yake ji game da mulkin jihar da kuma yadda zai tsayawa ‘yan Kano a yi musu aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.