Mataimakin Shugaban Barca Ya Tabbatar da Tattaunawa da Messi Kan Batun Dawowarsa Barcelona
- Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tabbatar da fara tattaunawa da Messi kan yadda zai dawo kungiyar
- A halin da ake ciki, Messi na can a PSG, inda yake kwasar kudade, kuma PSG din ma da kanta bata son ya tafi
- Mataimakin shugaban kungiyar Barca ya bayyana kadan daga dalilin da yasa suke son Messi ya dawo
Kasar Spain - Mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Rafa Yuste ya tabbatar da tuntubar Lionel Messi don duba yiwuwar dawowarsa kungiyar, Forbes ta ruwaito.
Messi dai ya fice daga Barca ne a 2021, inda ya tsallaka zuwa kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke kasar Jamus bisa yarjejeniyar zaman shekaru biyu.
Wa’adin zaman Messi a PSG zai cika ne a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa, lamarin da yasa Barca ke neman sake zawarcinsa.
PSG bata son Messi ya tsere ya tafi
Sai dai, ita kanta PSG din na son ci gaba da zaman Messi, kasancewar tun farko kungiyar ta ce akwai yarjejeniyar ya iya tsawaita zamansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kafar Mundo Deportivo ta ruwaito a ranar Juma’a cewa, PSG na son Messi ya tsaya, inda kungiyar tace za ta iya kara masa kudade masu yawa.
A ranar Alhamis, kafar labaran wasanni ta L’Equipe ta ruwaito cewa, Messi yana samun £3.375 a duk wata a kungiyar ta PSG.
A hakan, Messi ne na uku a masu samun zunzurutun kudade a kungiyar bayan Neymar da yake na biyu sai kuma Kylian Mbappe da ke kan gaba.
Dalilin da yasa Barca ke son Messi ya dawo
Da Yuste ke magana game da dawowar Messi, ya ce:
“Leo da ahalinsa sun san irin kaunar da nake matukar yi musu. Na shiga batun yarjejeniyar da aka yi wacce abin takaici bata kai ga nasara ba.
“Ina jin sukar kaya a gefe na cewa Leo ba zai ci gaba da wasa a kungiyarmu ba. Idan muna magana a kan La Masia da kuma kwallon kafa daga tushe, to muna magana ne kan Messi.
“Tabbas ina kaunar ya dawo saboda abin da hakan zai wakilta na wasa, abota da kuma tattalin arziki. Muna kan magana dashi, tabbas.”
Ronlado ya koma Al-Nassr ta Saudiyya
A wani labarin, kun ji yadda fitaccen dan kwallon kafan nan, C. Ronaldo ya koma buga wa wata kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya.
Wannan ya faru ne bayan da Ronaldo ya bar kungiyar kwallon kafan Manchester United da ke Ingila.
Ba sabon abu bane ‘yan kwallon kafa su koma kasashen larabawa don samun kudade masu kauri.
Asali: Legit.ng