Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Tayi Babban Kamu, Ta Cafke Wasu Miyagun Bata Gari a Jihar

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Tayi Babban Kamu, Ta Cafke Wasu Miyagun Bata Gari a Jihar

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu ɓata gari a jihar a cikin watan azumin Ramadana
  • Rundunar ta cafke ƴan fashi da makami, masu dillancin miyagun ƙwayoyi da ɓarayin kayayyaki a jihar
  • Rundunar ta bayyana cewa ba za tayi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta fatattaki duk wasu ɓata gari daga jihar

Jihar Kano- Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana cewa ta cafke mutum 14 da ake zargi da fashi da makami, dillancin ƙwayoyi da ɓarayi a cikin satin farko na watan azumin Ramadan.

Kakkarɓar ɓata garin wanda tawagar jami'an rundunar na 'Operation Restore Peace' suka gudanar, ya sanya an ƙwati muggan makamai, ƙwayoyi da kayayyakin sata. Rahoton Channels Tv

Yan Daba
Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Tayi Babban Kamu, Ta Cafke Wasu Miyagun Bata Gari a Jihar Hoto: Within Nigeria
Asali: UGC

A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa kwamshinan ƴan sandan jihar yace babu sauran saurarawa ga ƴan daba a jihar.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Babban Abinda Ya Sa Abba Gida-Gida Ya Lallasa APC a Zaben Gwamna a Kano

Rundunar tace tana cigaba da zage damtse wajen ganin ta raba jihar Kano da duk wasu laifuka da aikata su, musamman a cikin lokacin watan azumin Ramadana. Rahoton Within Nigeria

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kwamishinan ƴan sandan ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu ɗauke da wani makami, ko haramtattun ƙwayoyi a cikin watan azumin Ramadana zai faɗa komar ƴan sanda."
"Ya kuma yi ƙara ga ɓata gari da su tuba ko kuma su tattara kayansu su bar jihar gabaɗaya. Idan ba haka ba za a cafke su sannan su fuskanci fushin hukuma." A cewar sanarwar

Rundunar ƴan sanda ta kuma buƙaci al'ummar jihar da su kawo rahoton duk wani abu dake faruwa zuwa ofishin ƴan sanda na kusa da su, sannan kada su ɗauki doka a hannun su.

Ya kuma tabbatarwa da al'ummar jihar cewa rundunar za ta cigaba da sintiri ba ƙaƙƙautawa domin kakkaɓe ɓata gari a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Jindadin 'Yan Sanda Ta Ƙasa

Kotun Musulunci Ta Yanke Wa Barawon Rake Hukuncin Bulala 10 A Kano

A wani labarin na daban kuma, kotun shari'ar musulunci ta zartar da hukuncinta kan wani ɓarawon rake a jihar.

Kotun musuluncin ta bayar da umurnin ayi masa bulali goma masu kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel