Watanni 2 Kafin Ya Bar Ofis, ‘Yan Majalisa Sun Amince da Bukatar da Buhari Ya Kawo

Watanni 2 Kafin Ya Bar Ofis, ‘Yan Majalisa Sun Amince da Bukatar da Buhari Ya Kawo

  • Majalisar wakilan tarayya ta yi na’am da rokon shugaban Najeriya na kafa wasu gandojojin jeji
  • Yayin da Hon. Alhassan Ado Doguwa ya dauko maganar, abokan aikinsa sun yi na’am da shi
  • Gwamnati ta kebe dajoji 10 a kasar nan da aka haramtawa mutane cire wani arzikin cikinsu

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta amince da bukatar Muhammadu Buhari na kebe wasu wurare na musamman a matsayin gandun daji a kasar nan.

Jaridar The Cable ta ce an cin ma wannan matsaya ne bayan Hon. Alhassan Ado Doguwa ya gabatar da maganar a zauren majalisa a ranar Laraba.

Gandun jejin da majalisar tarayya ta kebe sun hada da jejin Allawa a Neja, jejin Apoi a Beyelsa, jejin Edumenum a Bayelsa da jejin Falgore da ke Kano.

Ragowar gandun da za a tanada su ne jejin Kogo a jihar Katsina, jejin Marhai a Nasarawa, jejin Oba da jejin Pandam da ke Filato a Arewa maso tsakiya.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru a Kujerar Minista, Pantami ya Fadi Barazanar da Najeriya ke Fuskanta

Za a samu gandu a Jigawa da Kwara

Haka zalika an ware jejin nan na Baturiya da ke Jigawa da na kamfe da yake yankin Kwara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da Hon. Doguwa ya bijiro da maganar, jaridar ta rahoto shi yana fadar a Nuwamban 2022, shugaban kasa ya ware wadannan jeji goma domin a kebe su.

'Yan Majalisa
Shugaban Majalisar Wakilai Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Idan har aka kebe wani daji a matsayin gandu, bai halatta wasu su rike sarar bisihoyinsa ko makamancin hakan, doka za ta kama masu faskararsa.

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan kasar ya ce Mai girma shugaban kasa ya fake da sashe na 18 na dokar gandun daji, ya aiko da takardar rokonsa.

Doka mai cikakken iko

Premium Times ta ce dokar ta ba shugaban kasa dama ya ayyana inda ya kamata ya zama gandun hukuma, kuma ya nada kwamitocin da za su kula da su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutum 24 Sun Mutu Yayin Da Wata Babban Mota Da Ta Tashi Daga Zaria Zuwa Legas Ta Yi Haɗari

Muhammadu Buhari ne yake da hurumin yanke wa’adin shugabannin gandun jejin.

Wannan bukata da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ta na kunshe cikin doka mai cikakken iko mai lamba ta 22 a gwamnatinsa ta kawo daga 2015.

Shari'ar Diezani Alison-Madueke

An samu labari cewa takardun koti daga ma'aikatar shari'ar ƙasar sun nuna cin hancin da aka ba Diezani Alison-Madueke domin ta bada kwangiloli.

A lokacin ta na Minista, Diezani Alison-Madueke ta bada kwangilolin miliyoyin daloli bayan ta karbi rashawar Kolawole Aluko da Olajide Omokore.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng