Gwamnan Legas Ya Sha, Ya Karbo Takardar Shaidar Lashe Zabe a Karo Na Biyu a Jiharsa

Gwamnan Legas Ya Sha, Ya Karbo Takardar Shaidar Lashe Zabe a Karo Na Biyu a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Legas ya karbi takardar shaidar lashe zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris da ta gabata a kasar nan
  • An ruwaito cewa, Sanwo-Olu na APC ne ya sake lashe zaben bana a Legas, zai sake mulkar jihar na tsawon shekaru hudu
  • Bayan karbar shaidar lashe zaben, gwamnan ya yiwa jama’arsa bayani, ya yi kira ga a zauna lafiya a mutunta juna

Jihar Legas - A ranar Alhamis 30 Maris, 2023 ne aka ba gwamnan jihar Legas shaidar lashe zaben gwamna a jihar bayan kammala zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ce ta ba gwamna Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat takardar, rahoton Punch.

Idan baku manta ba, Sanwo-Olu ya sake lashe zaben gwamna a jihar Legas a karo na biyu, inda ya lallasa ‘yan takarar PDP da Labour a zaben makon jiya.

Kara karanta wannan

INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

Sanwo-Olu ya karbi takardar komawa mulki
Gwamna Sanwo Olu lokacin da yake karbar shaidar lashe zabe | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A zaben, Sanwo-Olu na APC ya samu kuri’u 762,134, inda dan takarar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour ya samu 312,329.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wanda yazo na uku kuwa, Olajide Adediran na jam’iyyar PDP ne, inda ya samu kuri’u 62,449, kamar yadda sakamakon zaben ya nuna.

Gwamna Sanwo-Olu ya karbo takardar shaidan lashe zabe

A yau, gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa zuwa ofishin hukumar zabe ta INEC, inda suka karbi takardun shaidan lashe zaben na bana da zai ba su damar mulki na karin shekaru hudu, PM News ta ruwaito.

Da yake magana bayan karbar takardar shaidan, Sanwo-Olu ya sake jaddada kiransa ga wanzar da zaman lafiya da mutunta juna a jihar ta Legas.

Hakazalika, ya ce akwai bukatar mutane su yi hakuri da juna ta fuskar addini da kabila domin a zauna lafiya a mori juna.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Jigon PDP ya janye daga takara a zaben fidda gwamin gwamna a wata jiha

An ba DSS shawarin kame wadanda ke son kafa gwamnatin wucin gadi

A wani labarin, kunji yadda jam’iyyar APC da PDP suka bayyana bukatar a gaggauta daukar mataki kan wadanda ke kitsa hanyar kafa gwamnatin wucin gadi kafin rantsar da Tinubu.

A cewar PDP da APC, ya kamata a bayyana sunayen ‘yan siyasan tare da kamo su domin sun saba kundin tsarin mulkin Najeriya.

Baya ga haka, jam’iyyun sun bayyana nesanta kansu da wannan aiki na cin amanar kasa da ka iya lalata tafarkin dimokradiyya a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.