‘A Kame Atiku da Obi’: Fani-Kayode Ya Yi Martani Kan Zargin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi
- Ana ci gaba da cece-kuce kan ikrarin hukumar DSS na cewa, akwai masu kitsa hanyar kafa gwamnatin wucin gadi a Najeriya
- Femi Fani-Kayode ya yi tsokaci, ya ce kawai a kama Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP
- A rubutun da ya yada a Twitter, Kayode ya ce babu mamaki akwai hannun ‘yan jam’iyyar adawa a wannan shiri na kawo gwamnatin wucin gadi
Jigon jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yi kira ga kama ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun PDP da Labour; Atiku Abubakar da Peter Obi.
Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a martaninsa ga batun hukumar DSS na ranar 29 ga watan Maris na cewa akwai masu son kawo tsaiko ga gwamnati mai jiran gado.
A cewarsa, zargin kafa gwamnatin wucin gadi ba zai rasa nasaba da Atiku da Obi ba, don haka ya kamata a gaggauta kama su, rahoton Vanguard.
Ya nemi a kwamushe manyan ‘yan siyasa, Obi da Atiku
Kayode, a wani rubutun da ya yada a Twitter a ranar Alhamis, ya ce bai kamata a dauki batun da DSS din ta gabatar sako-sako ba saboda muhimmancinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, duk da ba a kafa gwamnatin wucin gadin ba, akwai yiwuwar a samu tsaiko da jefa Tinubu cikin barazana kafin rantsar dashi.
A cewarsa:
"A yanzu dai alamomin a bayyane suke kuma balo-balo cewa akwai wani sharri a kasa.
“Abin yabawa ne da kuma jinjinawa cewa DSS tana aikinta, daga karshe kuma ta ba da sanarwa jiya na abin da ke faruwa.”
A tun farko, hankali ya tashi bayan samun labarin yadda wasu ‘yan siyasa ke neman kawo gwamnatin wucin gadi kafin rantsar da Tinubu.
PDP da APC sun ce a bayyana sunayen masu kitsa sharrin
A bangare guda, jam’iyyun siyasan APC da PDP sun ce lokaci ya yi da DSS ya kamata ta sanar da duniya wadanda ke shirin kawo tsaiko ga tsarin.
Hakazalika, sun nemi a kama duk wani dan siyasa da ake zargin yana da hannu a tunanin kawo gwamnatin wucin gadin.
Wannan na bayyana cewa, jam’iyyun basu amince daya daga cikin mambobinsu ne mai kokarin kawo wannan lamari ga kasar nan ba.
Asali: Legit.ng