Bayan Shekaru a Kujerar Minista, Pantami ya Fadi Barazanar da Najeriya ke Fuskanta

Bayan Shekaru a Kujerar Minista, Pantami ya Fadi Barazanar da Najeriya ke Fuskanta

  • Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi jawabi a taro a kan muguwar illar yi wa shafukan yanar gizo kutse
  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya ya ce ya zama dole a yaki wannan barna
  • Pantami ya ce gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalar ba, sai kowa ya bada gudumuwarsa

Abuja - Isa Ali Ibrahim Pantami wanda shi ne Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, ya koka kan yawaitar masu kutse a shafukan yanar gizo.

A ranar Talata, The Cable ta ce Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya gabatar da jawabi wajen wani taron kwana biyu na karawa juna sani da aka shirya.

Ma’aikatar sadarwa ta tarayya da hadin gwiwar babban bankin Duniya su ka shirya taron masu ruwa da tsaki wajen kare shafin yanar gizo a Abuja.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana

Mai girma Ministan yake cewa yayin da ake ganin cigaban fasaha a Duniya, ana samun masu yi wa shafukan gizo kutse kusan dare da rana a kullum.

Isa Ali Ibrahim Pantami ya koka

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a jiya, Isa Ibrahim Pantami ya nuna wannan danyen aiki ya zama cikas ga kamfanoni da kasuwanci a Duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Pantami ya ce yadda bangaren tattalin arzikin zamanin Najeriya yake tasowa a yau, akwai matukar bukatar ba shi kariya da miyagun da ke aika-aika.

Pantami
Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Hakan ya sa Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga masu uwa da makarbiya a harkar da su bada gudumuwa wajen tsare shafukan gizo.

A jawabin da ya gabatar, Ministan ya nakalto wani rahoto na barnar da ake yi a Afrika, ya ce a bana, karuwar barna a shafin gizo ya karu da 300%.

Kara karanta wannan

Ka kawo karshen yunwa da fatara: Kungiyar Musulmai ta roki Tinubu alfarma idan ya karbi mulki

Abin ya kai inda ya kai a yau

Punch ta ce ganin yadda lamarin ya tabarbare, Ministan sadarwar kasar ya ce abin ya kai matakin da za a damu, ya bukaci kowa ya taka rawar ganinsa.

Bankin Duniya ya yi hasashen darajar tattalin arzikin zamanin Afrika zai kai $180b nan da 2025, hakan ya nuna za a samu damamaki da cigaba a nahiyar.

Domin a bada kariya aka fito da dabaru a 2022, har ta kai aka kafa hukumata musamman ta NDPB, amma Ministan ya ce gwamnati kadai ba za ta iya ba.

Canjin Gwamnati a Najeriya

An fara shirye-shiryen mika mulki a Najeriya, rahoto ya zo cewa kwamitin PTC ya karbi mutanen Bola Tinubu a matsayinsa na zababben shugaban Kasa.

Sakataren gwamnatin tarayya wanda shi ne shugaban PTC na kasa ya bada wannan sanarwa, ya ce Tinubu ya bada sunan Gwamnan Kebbi da Wale Edun.

Kara karanta wannan

Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng