Ina Jiran Hukuncin Da Kotun Sauraren Shari'ar Zaɓe Zata Yanke Kafin Na Cika Alƙawari na Nabarin Najeriya

Ina Jiran Hukuncin Da Kotun Sauraren Shari'ar Zaɓe Zata Yanke Kafin Na Cika Alƙawari na Nabarin Najeriya

  • Kafin ayi zaɓen shugaban ƙasar Najeriya, Bode George ya taɓa alƙawari, inda yace idan Tinubu yaci zaɓe zai fita daga Najeriya ya koma wata ƙasa
  • Tun bayan da INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ba'a ji ɗuriyar Bode George ba
  • Tsohon sojan kuma gogaggen ɗan siyasar, ya magantu, inda yace yana nan akan maganar sa ta barin Najeriya, amma ya tsaya da batun har sai abinda hukuncin kotu yace abisa zaɓen

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Bode George yace zai tsaya ya ga abin da ya ture wa buzu naɗi dangane da shari'ar da ake ta shugaban ƙasa wacce Tinubu ya lashe zaɓe kafin yabar Najeriya.

Bode George ya bayyana haka ne a wani hira da yake yi da gidan talabijin na "Arise News" mai taken "The morning show".

Kara karanta wannan

Matashiya: Yadda Jami'ar Chicago ta Tabbatar da Cewa Makarantar Tinubu Ya Halarta

Idan za'a iya tunawa, Bode George yayi alƙawarin cewar, in har Asiwaju Bola Tinubu na APC yaci zaɓe, zai bar Najeriya.

Hakan kuwa akayi, domin tuni jam'iyyar ta APC da Asiwaju Bola Tinubu ke wa takara, ta samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa da akayi 25 ga watan Fabrairu.

Bidee
Ina Jiran Hukuncin Da Kotun Sauraren Shari'ar Zaɓe Zata Yanke Kafin Na Cika Alƙawari na Nabarin Najeriya
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen, Bode George yace yana nan akan bakan sa na komawa wata ƙasar domin ci gaba da rayuwa.

A cewar sa:

"Saura kaɗan na kai shekaru 80, Ina da damar na zaɓi duk inda nake so naje na ƙarasa rayuwa ta cikin salama."

Ya ƙara da cewa:

"Sojan Ruwa ne ni kafin nayi ritaya, duk rayuwa ta nayi tane ina ta zagaye ƙasashen duniya, ina da damar zuwa duk inda yayi mun domin inyi rayuwa ta cikin aminci.

Kara karanta wannan

Kujerar Sanata: Gwamnan PDP Da Yasha Kasa Ya Rungumi Kaddara, Yayi Bayani Mai Ratsa Zuciya

"Zan tafi ƙasar da take da ruwan sha, wutar lantarki, tsaro da abinci", inji shi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Bode George yana cewa:

"Abinda nake buƙata kenan domin ƴaƴa na da jikoki na. Abinda ya kamata nayi yanzu shine, na daina harkar siyasa, nabar jam'iyya ta".
"Saboda a shekaru na 25 danayi a fagen siyasa ba abinda nake sai gwagwarmayar ganin ƙasar nan ta gyaru"
"Amma idan na tafi, zan yanke hukuncin abinda nake so. Wasan ba'a tashi ba. Zan jira hukuncin kotu akan lamarin. Hakan kuma baya nufin bazan sake dawowa Najeriya bane".
"Idan nace zan fita daga Najeriya, ko bazan koma ba, aiki zanje na nema? Babu wanda zai ɗauke Ni aiki," inji shi

Rundunar Ƴan Sandan Najeriya Ta Samu Nasarar Ƙwato Mutane Da Masu Garkuwa Da Mutane Suka Ƙwamushe a Kogi

Hukumar zaratan ƴan sandan Najeriya sun samu nasarar ƙwato wasu mutane guda goma sha uku waɗanda wasu maras ta ido da ake zaton ƴan bindiga ne suka Ƙwamushe su acan jihar Kogi.

Kara karanta wannan

"Gwamnati a Ƙarƙashin Jagorancin Tinubu Zata Kasance Mai Tasiri ga Rayuwar Ƴan Najeriya" – Buhari

An ruwaito cewar, sai da rundunar ƴan sanda reshen jihar Kogi, suka yi bata kashi da ɓata garin, kafin daga bisani ayi nasara akan mugayen.

Biyo bayan harin ne, hukumar ƴan sandan jihar ta Kogi, suka buƙaci mazauna yankin Eleite dasu kwantar da hankalin su, inda suka ce, sukai rahoton duk wanda suka gani da rauni yana neman magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

Online view pixel