Ma’aikata Sun Fadi Sabon Farashin da Man Fetur Zai Koma Ana Janye Tallafi a Bana

Ma’aikata Sun Fadi Sabon Farashin da Man Fetur Zai Koma Ana Janye Tallafi a Bana

  • Shugaban Kungiyar PENGASSAN ya nuna farashin man fetur zai koma tsakanin N360 da N400
  • Bayan taron NEC da aka yi a Abuja, Kwamred Festus Osifo ya yi magana a kan cire tallafin fetur
  • PENGASSAN ta goyi bayan gwamnati ta daina biyan tallafin fetur da sharadin za a gyara matatu

Abuja - Kungiyar nan ta PENGASSAN ta manyan ma’aikatan fetur da gas a Najeriya, ta ce za a samu canjin farashi idan aka cire tallafin man fetur.

The Cable ta rahoto Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo ya na mai cewa za a tsinci farashin lita tsakanin N360 da N400 idan aka daina biyan tallafi.

Osifo ya zanta da manema labarai ranar Talata a garin Abuja, bayan sun tashi taron majalisar NEC.

Shugaban kungiyar ma’aikatan yake cewa idan gwamnati ta cire hannu daga biyan tallafin man fetur, darajar Dala ne zai yi tasiri a kan farashinsu.

Kara karanta wannan

2023: An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai

Darajar Dalar Amurka a kasuwa

An ji Osifo yana cewa a yau kusan NNPC ne kurum yake shigo da mai, kamfanin yana lissafi ne da farashin da ya samu Dalar Amurka a hannun CBN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan aka yi la’akari da darajar Naira a kasuwar canjin kudin kasar waje, PENGASSAN ta ce bankin CBN yana saidawa NNPC Dala ne a kan N400-N450.

Fetur
Budurwa a gidan man fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Saboda haka idan aka cigaba da tafiya a haka, kimanin N360 zuwa N400 za a saida litar fetur.

Matsayar da PENGASSAN ta dauka

Tashar talabijin nan na Channels ta rahoto shugaban kungiyar yana cewa sun bada umarni ga ‘ya‘yansu da su fito da man fetur ko a karbe masu lasisi.

Kwamred Osifo ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta gyara matatun kasar, ya ce hakan zai jawo kayan mai suyi sauki, sannan jama’a su samu abin yi.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

PENGASSAN ta na goyon bayan gwamnati ta cire hannunta daga harkar mai, amma ta na so a gaggauta gyara matatun da ake da su na tace danyen mai.

Dole ne gwamnati da za ta karbi mulki ta duba batun canjin takardun kudi da wahalar fetur, sannan Osifo ya ce sai an yi tanadi idan aka cire tallafi.

Taimakon gaggawar kasar Saudi

Rahoto ya zo a baya cewa cibiyar nan ta KSrelief ta Saudi Arabiya ta aiko da shinkafa, wake, tumaturi da mai da sauran kayan abinci domin rabawa jama’a.

Hukumar NEMA da hadin-kan jami’an SEMA sun raba kayan a wasu garuruwan da ke Kano. Wadanda masifa ta auka masu a baya suka amfana da kayan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng