Mummunan Gobara Ta Tashi A Fitacciyar Kasuwa A Legas, Bidiyo Ya Fito
- Wasu sassan daya cikin manyan kasuwanin jihar Legas, da ke Lagos Island, a halin yanzu yana ci da wuta
- A cewar rahotanni, gobarar ya shafi wani plaza da ke kasuwar Balogun amma an tura jami'an hukumar kashe gobara daga bangarori biyu zuwa wurin da abin ya faru
- Da ya ke martani, Jubril A. Gawat, hadimin gwamnan Jihar Legas kan sabuwar kafar watsa labarai ya bayyana cewa an shawo kan gobarar, an dakile yaduwarta zuwa wasu sassa
Jihar Legas - Gobara ta yi barna a fitacciyar kasuwar Balogun da ke Legas Island a ranar Talata, 28 ga watan Maris na 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta shafi wani rukunin shaguna inda ake sayar da takalman mata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An tura jami'an hukumar kashe gobara su kai dauki a kasuwar
Jami'in hukumar kashe gobara daga bangarori biyu a Legas sun isa wurin don kashe gobarar.
An yi gobara daban-daban a kasuwar, inda aka rasa dukiyoyin miliyoyin naira.
Hadimin Gwamna Sanwo-Olu ya yi martani
Da ya ke martani kan afkuwar lamarin a shafinsa na Twitter, Jubril A. Gawat, @Mr_JADs, babban mataimaki na musamman (SSA) ga gwamnan jihar Legas kan sabuwar kafar watsa labarai, ya ce jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin.
A wani wallafa a Twitter da Legit.ng ta gani a ranar Talata, Gawat @Mr_JAGs ya rubuta:
Sanarwa kan gobara
"Hukumar kashe gobara da ceto na jihar Legas a halin yanzu suna can suna fafatawa da wuta a Kasuwar Balogun wacce ta shafi saman gidan mai bena biyar.
"Amma dai an yi galaba kan wutar don an dakile ta daga yaduwa."
Bidiyo ya fito
A bangare guda, wani mai amfani da shafin Twitter, D Obidient Son, @grayjoy69, ya wallafa bidiyon gobarar da ke faruwa a kasuwar Balogun.
Kalli bidiyon a kasa:
Wata mummunan gobara ta lakume shaguna guda 80 a babban kasuwar jihar Kano
A wani rahoton mai kama da wannan kun samu rahoton cewa mummunan gobara ta tashi a kasuwar Kurmi da ke birnin Kano a ranar Laraba 1 ga watan Maris.
Gobarar ta lakume shaguna a kalla 80 a cewa mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi a wata sanarwa da ya fitar dangane da afkuwar lamarin.
Asali: Legit.ng