Allah Ya Yiwa Daya Daga Cikin ’Yan Majalisun Imo, Arthur Egwim Rasuwa Jiya Litinin
- An samu mummunan labarin rasuwar dan majalisar wakilai a jihar Imo bayan wata jinya da ya yi a kasar waje
- Rahoto ya bayyana kadan daga tarihin aikinsa da kuma gwagwarmayarsa ta siyasa tun daga 2015 zuwa yanzu
- Majiya ta ba da labarin yadda aka tallafa wajen kai shi kasar waje domin yi masa jinya, amma bai tsira daga cutar ba
Jihar Imo - Daya daga cikin fitattun ‘yan majalisar dokokin jihar Imo, Hon. Arthur Egwim ya kwanta dama, rahoton jaridar The Nation.
Dan majalisar da ya fito daga yankin Orlu ya rasu ne a jiya Litinin 27 ga watan Maris bayan jinyar cutar daji.
An zabe shi ne a karon farko zuwa majalisar a karkashin inuwar jam’iyyar APC a 2015, inda ya sake samun damar shiga majalisar a 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar AA.
Dani za a yi: Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa
Mukaman da ya rike a majalisa
Ya kasancewa shugaban kwamitin kudi da asusun gwamnatin jihar a majalisar dokokin ta Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ya kasance shugaban kwamitin harkar masarautu da harkokin al’umma , hakazalika shugaban kwamitin shari’a a majalisar.
Arthur Egwim ya kasance dan takarar majalisar tarayya a karkashin inuwar jam’iyyar APGA a mazabar Ideato a zaben 2023.
Sai dai, ya fadi a zabe, inda dan takarar jam’iyyar PDP, Ugochinyere Imo ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu.
Yadda aka kai shi kasar waje jinya
A cewar wata majiya daga jaridar The Street Journal, dan majalisar ya kasance a kasar waje na wani dan lokaci yana jinya kafin daga bisani rai ya yi halinsa.
A cewar majiyar:
“An shilla dashi kasar waje don yi masa aiki amma bai tsira ba. Gwamnatin jihar ce ta tallafa masa wajen neman magani a kasar waje. Tabbas abin jimami ne.
“Ya kasance dan majalisa mai kokari kuma mai mutunta kowa, daidai lokacin da yake kokarin mika wa zababben dan majalisa a watan Yuni, ya tafi.”
A jihar ta Imo cikin makon nan aka kashe wasu jami'an tsaron hukumar NSCDC a lokacin da suka bakin aiki.
A cewar rahoto, baya ga kashe jami'ai uku, an kuma hallaka wasu fararen hula biyu da ke wucewa.
Asali: Legit.ng