Gwamna Wike Ya Bayyana Abinda Zai Yi Bayan Ya Sauka Daga Mulki

Gwamna Wike Ya Bayyana Abinda Zai Yi Bayan Ya Sauka Daga Mulki

  • Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana cewa ba zai fice daga ƙasar nan ba idan wa'adin mulkin sa ya ƙare
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne yayi da yake martani kan barazanar da shugaban EFCC yayi na cewa zasu cafke wasu gwamnoni bayan ranar 29 ga watan Mayu
  • Wike ya ƙara da cewa ko kaɗan bai da damu da barazanar ta EFCC ba, inda ya ƙara da cewa a shirye yake ya amsa goron gayyatar su

Port Harcourt, Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa a cikin ƙasar nan bayan wa'adin mulkin sa ya cika a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A cewar rahoton New Telegraph, gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan bayanin da shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa yayi na cewa hukumar za ta cafke gwamnonin da ake zargi da cin hanci bayan wa'adin mulkin su ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Taron Biki Ya Tarwatse Bayan Amarya Ta Gano Wani Babban Sirrin Ango, Bidiyon Ya Yadu

Gwamna Wike
Gwamna Wike Ya Bayyana Abinda Zai Yi Bayan Ya Sauka Daga Mulki Hoto: Twitter/nyesomwike
Asali: Facebook

A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Tv a safiyar ranar Litinin, gwamnan yace zai karɓi goron gayyatar EFCC idan suka neme shi bayan ya sauka daga kan mulki.

Wike ya ƙara da cewa barazanar da Bawa yayi ta cafke gwamnoni bayan wa'adin mulkin su ya cika, kwata-kwata bata dame shi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akwai raɗe-raɗin dake yawo cewa Wike yana ɗaya daga cikin gwamnonin da EFCC ta sanyawa ido, saidai gwamnan yace ba inda zai je bayan wa'adin mulkin sa ya cika.

A kalamansa:

"Ba zan gudu ba saboda EFCC. Meyasa za su gayyace ni? Idan suka gayyace ni, zan amsa gayyatar su. Ba zan gudu ba."

Wike yana ɗaya daga cikin manyan gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) masu ƙarfin faɗa a ji a babban zaɓen 2023.

Ya jagoranci tawagar gwamnoni biyar na jam'iyyar PDP da suka yiwa shugabancin jam'iyyar bore bayan sun ƙi bari shugabancin jam'iyyar ya koma Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara

Rikicin PDP: Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Akayi Masa

A wani labarin na daban kuma, shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu, yayi watsi da dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar ta PDP ya bayyana waɗanda sune kaɗai ke da alhakin dakatar da shi daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng