Kungiyar CAN Ta Janyo Hankalin Al'ummar Jihar Adamawa Game Da Zaben Cike Gurbi

Kungiyar CAN Ta Janyo Hankalin Al'ummar Jihar Adamawa Game Da Zaben Cike Gurbi

  • Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) tayi muhimmin kira ga al'ummar jihar Adamawa yayin da ake tunkarar zaɓen cike gurbi a jihar
  • Ƙungiyar ta buƙaci al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu su sake fitowa domin gudanar da zaɓen
  • Ƙungiyar ta CAN ta kuma yi kira ga shugabannin addinai a jihar da su cigaba da bin doka da oda

Jihar Adamawa- Ƙungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Adamawa, tayi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankulansu sannan su dawo da ƙwarin guiwar da suke da shi akan hukumar zaɓe (INEC) domin gudanar da zaɓen cike gurbi a jihar.

Shugaban ƙungiyar reshen jihar, Stephen Mamza, shine yayi wannan kiran yayin tattaunawa da manema labarai ranar Lahadi a birnin Yola. Rahoton Premium Times

Adamawa CAN
Kungiyar CAN Ta Janyo Hankalin Al'ummar Jihar Adamawa Game Da Zaben Cike Gurbi Hoto: Gazettengr
Asali: UGC

Rabaran Mamza, ya bayyana cewa a matsayin su na shugabannin kiristoci a jihar, sun yi dukkanin ƙoƙarin da za suyi domin ganin mutane sun fito sun kaɗa ƙuri'un su saboda alƙwarin da INEC tayi na gudanar da sahihin zaɓe.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Mutane 79 da Suka Haddasa Rikici da Karya Doka Yayin Zaɓen Gwamna A Jihar Arewa

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna kira ga mutane da su kwantar da hankulansu sannan su dawo da ƙwarin guiwar da suke da shi kan INEC na cin gashin kanta, ƙwarewa, gaskiya da adalci wajen kula da ƙuri'un jama'a yayin da muka tunkari zaɓen cike gurbi."
"Muna kuma kira da babbar murya kan jami'an da tsaro da kafafen watsa labarai da kada su bari matsin lamba yayi tasiri a kan su yayin da suke lura da abubuwan dake faruwa a zaɓen tun daga kaɗa ƙuri'a, tattara sakamako da kuma liƙa sakamakon zaɓen."

Shugaban ƙungiyar ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su manta da siyasa su mayar da hankali wajen ganin mutanen jihar sun cigaba da haƙuri da mutunta juna a tsakanin su. Rahoton Gazettengr

Ya kuma yi kira kan mutanen jihar musamman shugabannin addinai da matasa da su cigaba da bin doka da oda.

Kara karanta wannan

INEC na Fuskantar Matsin Lamba Akan ta Ƙara Duba Sakamakon Zaɓen Gwamnan Kano, Kaduna da Ogun

Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

A wani labarin na daban kuma, wasu ƴan siyasa a Najeriya na tsaka mai wuya kan kalaman su a lokacin zaɓe.

Ƙasar Ingila ta ƙaƙaba musu takunkumi saboda iriin kalaman da suka riƙa furtawa akan zaɓen ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng