Oladipo Diya: Lokacin Da Marigayi Sani Abacha Ya Kama Mataimakinsa Kan Juyin Mulki Na 1997, Duba Bidiyon

Oladipo Diya: Lokacin Da Marigayi Sani Abacha Ya Kama Mataimakinsa Kan Juyin Mulki Na 1997, Duba Bidiyon

  • Janar Oladipo Diya, tsohon shugaban ma'aikatan fadar marigayi Janar Sani Abacha, ya rasu a safiyar ranar Lahadi
  • Idan za a iya tunawa tsohon shugaban mulkin sojan ya kama mataimakinsa, Diya, kan zarginsa da hannu a juyin mulki na 1997
  • Wani bidiyoda ke nuna lokacin da ake shari'arsa ya yadu jim kadan bayan dansa Barista Oyesinmilola Diya, ya sanar da rasuwarsa a madadin iyalin

Oladipo Diya, tsohon shugaban ma'aikatan fadar marigayi shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya rasu yana da shekaru 78.

Diya ya mutu a safiyar ranar Lahadi, 28 ga watan Maris, bayan dansa Barista Oyesinmilola Diya, ya sanar da rasuwarsa, a madadin iyalan.

Diya da Abacha
Bidiyon lokacin da Abacha ya kama matamakinsa Diya kan zargin cin amanar kasa. Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da ke faruwa game da Oladipo Diya, Sani Abacha, Sojojin Najeriya a baya-bayan nan

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Game Da Tsohon Hafsan Hafsoshin Soji Na Zamanin Abacha, Laftanar Janar Diya

Barista Oyesinmilola Diya, cikin sanarwarsa, ya bukaci al'umma su saka iyalansa a addu'a yana mai cewa za a sanar da tsarin yadda za a birne marigayin nan ba da dade wa ba.

Diya na cikin janar din soji da gwamnatin Abacha ta kama a 1997 kan juyin mulki kuma aka same shi da laifi a 1998.

A cikin mutane 14, an yanke wa janar din hukuncin kisa a watan Afrilu, amma, Abacha ya rasu kafin a zartar da hukuncin, kuma Janar Abdulsalami Abubakar ya musu afuwa.

Dalilin da ya sa Abacha ya kama Dipo Diya

Bidiyon lamarin da shafin instagram na @onlyinnigeria ya wallafa, da Gidan Talabijin na Kasa, NTA, ya nada ya yadu.

An yi wa bidiyon da lakabi kamar haka:

"Bidiyon lokacin da Shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha ya kama mataimakinsa, Janar Oladipo Diya da wasu kan zargin juyin mulki a 1997 kuma aka same su da laifin cin amanar kasa sannan aka yanke musu hukuncin kisa a 1998.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Mataimakin Shugaban Kasa Ya Mutu

"A ranar 8 ga watan Yunin 1998, Abacha ya rasu a wani mai daure hankali.
"Bayan Abacha ya mutu kafin ranar zartar da hukuncin, gwamnatin Abdulsalami Abubakar ta rage hukuncin kuma aka saki janar din."

Abubuwa bakwai masu muhimmanci kan, Oladipo Diya, tsohon hafsan hafsoshin soji na zamanin Abacha

A ranar Lahadi, 26 ga watan Maris ne Allah ya yi wa Oladipo Diya, tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin mulkin soja a zamanin marigayi Janar Abacha ya riga mu gidan gaskiya.

Ya rasu saura kwanaki kadan ya cika shekaru 79 a duniya.

Dansa, Barista Oyesinmilola Diya, shine ya sanar da rasuwar mahaifinsa a madadin yan uwansa, inda ya bukaci yan Najeriya su taya su addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel