Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Harbe Jami’an Tsaro a Jihar Enugu
- An samu wani mummunan yanayi a jihar Enugu, inda aka harbe wasu jami’an ‘yan sanda har biyu nan take
- Rahoto ya bayyana cewa, an harbe jami’an ne a lokacin da suke bakin aiki a wani yankin jihar da ke Kudu
- Ana yawan samun tashin hankali da kisan jami’an tsaron Najeriya a Kudu maso Gabashin Najeriya
Jihar Enugu - Bayan kwanaki kadan na sararawa, ‘yan bindiga sun sake kai garmaki kan jami’an tsaro da ke aiki a jihar Enugu, an kashe ‘yan sanda biyu, Daily Post ta tattaro.
Wannan harin ya faru ne da misalin karfe 12 na rana a wurin binciken ‘yan sanda da ke tsakanin kasuwar Kenyatta da jami’ar Najeriya da ke Enugu.
Wata majiya ta shaida cewa, an farmaki ‘yan sandan ne da ke aikin binciken ababen hawa, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta, inda aka ga jami’an ‘yan sandan biyu na kwance cikin jini a kwalbati.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Enugu bata yi martani game da aukuwar wannan mummunan lamarin ba.
An hallaka ‘yan sanda a jihar Taraba
A bangare guda, yanayi irin wannan ya faru a jihar Taraba, inda wasu sojoji suka bindige jami’an ‘yan sanda har biyu nan take.
Wannan ya faru ne a cibiyar hukumar zabe mai zaman kanta a lokacin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar a makon da ya gabata.
Kammala zaben gwamnan jihar Taraba dai ya zo da tsaiko, wanda ya kai ga jinkirin sanar da wanda ya lashe zaben har zuwa wani dan lokaci bayan aukuwar lamarin.
An hallaka ‘yan ta’adda 60 a jihar Borno
A wani labarin kuma, kun ji yadda sojojin Najeriya suka hallaka ‘yan ta’addan da suka so kawo tsaiko ga tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Wannan na faru ne awanni kadan bayan da gwamnan jihar, Babagana Zulum ya kada kuri’arsa a mazabar da yake zabe.
A cewar majiya, akalla ‘yan ta’adda 60 ne suka mutu, inda wasu kuma suka samu munanan raunuka. An kuma kwato kayayyakin aikata laifi, ciki har da mota daga hannun masu tada kayar bayan a Borno.
Asali: Legit.ng