Baya Ga Dangote, an Fara Samun Sabbin Attajirai da Ke Tasowa a Nahiyar Afrika

Baya Ga Dangote, an Fara Samun Sabbin Attajirai da Ke Tasowa a Nahiyar Afrika

  • An samu sabbin attajirai masu biliyoyin daloli a nahiyar Afrika da ke harkallar kasuwanci daban-daban
  • Wadannan attajirai sun fito ne daga Afrika, kuma suna taka rawar gani a jerin masu kudi a duniya a wannan shekarar
  • Wasu daga cikinsu suna sana’ar da ta shafi yanar gizo, wasu harkar sufuri da dai sauran harkalloli na halas

Nahiyar Afrika na ci gaba da samun sabbin masu kudi da ake ji dasu a duniya duk kuwa da yadda farashin dala ke kara shillawa sama.

Forbes ta ruwaito cewa, nahiyar Afrika na da attajiran da ake ji dasu a duniya akalla 46, kuma nan da shekaru 10, dukiyar daidaikun jama’a a nahiyar zai habaka zuwa 30%.

Business Insider ta ruwaito cewa, nahiyar na da attajirai masu biliyoyi da ke tasowa da adadin kudi mai yawa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Yadda ake samun sabbin attajirai a Afrika
Dangote da sauran attajiran da ke tasowa a Afrika | Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Wadannan daidaikun attajiran na fitowa ne daga fannin kasuwanci daba-daban, ciki har da fasahar zamani da gine-gine.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mohamed Mansour: $2.9bn

Attajirin mai kudi dan kasar Masar, Mohamed Mansour ya fara kasuwanci ne irin na gidansu karkashin kamfanin Mansour Group.

Kamfanin ya mai da hankali ne ga fannin motoci da kuma harkallar siye da siyarwa na kayayyaki daban-daban.

Koos Bekker: $2.6bn

Ya fara kasuwanci ne a fannin da ya shafi yada labarai a kamfaninsa mai suna Naspers da ke da hannun jari a manyan kamfanoni a duniya, ciki har da Tencent da WeChat.

Mohammed Dewij: $1.5bn

Dewij ne shugaban kamfanin METL Group a Tanzania, ya kasance hamshakin attajiri kuma mai kamfanin harkar noma, samar da kayayyakin yau da kullum da gine-gine.

Dewij sananne a fannin noma da harkar gine-gine, hakazalika ya yi shuhura wajen aikin hidima ga al’umma a karkashin Mo Dewij Foundation da ke ba da tallafi a fannin ilimi, lafiya da ci gaban al’umma a Tanzania.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Yasseen Mansour: $1.1bn

Yasseen hamshakin attajiri ne dan kasar Masar, wanda ke tare da ‘yan uwansa a karkashin kasuwancin hadaka na Mansour Group da ke mai da hankali kan harkar motoci, sufuri da gine-gine.

Michiel Le Roux: $1.2bn

Michiel Le Roux tsohon ma’aikacin banki ne da ke da tarin kudin da suka kai $1.2bn, kuma sananne a wannan fannin na hada-hadar kudi ta banki.

Le Roux ne daya daga cikin mamallakan bankin Capitec da ke cike gurbin sashen kudi da banki a yankunan da babu bankuna.

Yayin da nahiyar Afrika ke samun habaka, za a ci gaba da samun attajirai masu tasowa daga nahiyar mai yawan jama’a da ke fama da fatara.

Dangote ne ke kan gaba

A bangare guda, hamshakin dan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote ne na daya a jerin attajiran Afrika na tsawon shekaru 12 kenan yanzu.

Dangote dai sananne wajen hada-hadar kasuwancin siminti, sikari da kayan abinci, inda daga baya ya kafa matatar mai man fetur mai iya tace ganga 65,000.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Ceto Mutum 201 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Borno Da Kaduna

A cewar rahoton Bloomberg, Dangote na da kudin da sun kai $19.7bn, kuma shi ne na 83 a jerin attajiran duniya.

Dangote dai na ci gaba da cin riba daga fannin kasuwancinsa, hakan na kara yawan dukiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.