Sojoji Sun Ceto Mutum 201 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Borno Da Kaduna

Sojoji Sun Ceto Mutum 201 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Borno Da Kaduna

  • Sojoji sun ceto mutane da dama da suka fada hannun masu garkuwa da mutane a sati biyu da suka gabata a jihohin Borno da Kaduna
  • Janar Musa Danlami, mai magana da yawun rundunar soji ne ya bayyana haka a zaman bayar da rahoto da hukumar ke yi duk sati biyu
  • An kuma hori sojojin da su cigaba da kasancewa cikin shiri don tabbatar da sun kawo karshen rayuwar yan ta'addan ISWAP da Boko Haram

Akalla mutum 201 da aka yi garkuwa da su a sati biyu da su ka gabata sojoji suka yi nasarar kubutarwa a atisaye daban-daban a jihohin Borno da Kaduna, rahoton Channels Television.

Babban darakta, mai kula da sashen watsa labarai, Manjo Janar Danlami ne ya bayyana haka a zaman tattaunawar da hedikwatar tsaro ke yi duk sati biyu ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tinubu: Minista Ya Rubutawa DSS Wasika, Ya Nemi a Cafke Peter Obi da Baba Ahmed

Sojojin Najeriya
Sojoji sun ceto mutane 201 daga hannun masu garkuwa a Borno, Kaduna. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manjo Janar Musa Danlami ya kara da cewa jami'an atisayen Whirl Stroke sun kashe yan ta'adda 14, sun kama kayan yan ta'adda 12 tare da ceto farar hula 16.

A gefe guda, babban jami'in da ke kula da shiyya (GOC) 7 kuma kwanmandan atisayen HADIN KAI, Manjo Janar Waidi Shuaibu, ranar Talata, ya kai ziyarar aiki ga bataliyyar hadin kwiwar 112, MAFA, Jihar Borno.

Ya yaba tare da jinjina kokarin jami'an na wargaza shirin wani da ISWAP ta shirya tsakar dare akan garin da dukun dukun safiyar Lahadi.

Janar Shuiabu ya jinjinawa sojoji bisa kokarinsu

Janar Shuaibu yayin ziyarar ya yaba wa jajircewa da salon yakin jami'an a lokacin bata kashin, ya na mai cewa jajircewarsu shi ne abin da aikin soja ke bukata.

Ya yabawa kokarin rundunar da su tsaya iya kare garin Mafa ba har da kakkabe maharan tare da hadin gwiwar jami'an jirgin yaki na atisayen Hadin Kai wanda hakan ya janyo guduwar duk wani tan ta'adda.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Ya kuma yi amfani da ziyarar don rokon jami'an na shiyya ta 7 da kuka atisayen Hadin Kai da su zama cikin shiri a ko da yaushe don maganin ragowar yan ta'addan ISWAP da Boko Haram a yankin.

Yan Hisbah sun shiga daki-daki don neman masu yin ayyukan badala a Kano

Hisbah a Kano sun yi wan bincike inda suka rika shiga daki-daki a Hills and Valley, wani wurin bude ido da shakatawa a unguwar Dawakin Kudu da ke Kano.

Kamar yadda jaridar intanet ta Sahara Reporters ta rahoto, sun yi wannan bincike ne da nufin kama masu badala a cikin dakunan, inda jami'an Hisaban suka tilastawa ma'aikatan wurin su zagaya da su daki-daki a gine-ginen da ke wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164