Wata Sabuwa: Ana Fargabar Sheƙe Mutane Biyu Bayan Yan Jagaliya Sun Kai Hari Ofishin Jam'iyyar APC na Zamfara

Wata Sabuwa: Ana Fargabar Sheƙe Mutane Biyu Bayan Yan Jagaliya Sun Kai Hari Ofishin Jam'iyyar APC na Zamfara

  • Zaɓen gwamnonin jihohi 28 na Maris ya samu tasgaro na rigime rigime, kwacen akwatu, da kuma yin amfani da ƴan jagaliya domin haddasa rikici
  • Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohi 28 da aka gudanar da zaɓukan gwamnoni asabar ɗin data gabata
  • Baya ga rasa rayuka, jigo a jam'iyyar APC yace yanayin yadda Ofishin APC ya lalace baza'a iya ƙiyasta adadin kuɗin da aka lalata a wajen ba

Zamfara - Rahotanni maras daɗin ji daga jihar Zamfara dake fitowa ya nuna yadda aka shiga jimami da damuwa sakamakon wani hari da yan jagaliya suka ƙaddamar a ofishin jam'iyyar APC dake Gusau, babban birnin jihar.

Rahoton ya sanar da yadda wasu mutane biyu suka rigamu gidan gaskiya sakamakon kaddamar musu da akayi yayin harin na bata garin.

Kara karanta wannan

Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewar, lamarin ya faru ne ranar Litinin ɗin data gabata, lokaci ƙadan bayan INEC ta saki sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Zamfara
Wata Sabuwa: Ana Fargabar Sheƙe Mutane Biyu Bayan Yan Jagaliya Sun Kai Hari Ofishin Jam'iyyar APC na Zamfara Hoto: Channelstv
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sakamakon da INEC ta saki na gwamnan jihar ta Zamfara dai ya nuna cewa, Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaɓen jihar ta Zamfara.

Jami'in kula da yaƙin neman zaɓen Tinubu/ Shetima na Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, lokacin da yake Allah wadai da faruwar lamarin.

Rahotanni sun nuna yadda maharan suka lalata ginin ofishin da abinda ke ciki, suka yagalgala sili, tayils, rufin ginin, abin hawa, janareto, kujeru, tilabishin da dadai sauransu.

Bayan duba yanayin yadda wajen ya lalace, Marafa yace bazai iya ƙiyasta adadin kuɗin da aka lalata a wajen ba.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

A cewar sa:

"Bayan kammala gamida sakin sakamakon zaɓe na 18 ga watan Maris, an ayyana PDP a matsayin waɗanda suka yi nasarar lashe zaɓen. Sai kuma da safe muka samu kira an afkawa ofishin mu har an lalata shi, awa biyu da ta wuce ba abinda nake sai dubawa." inji shi.

Jigo a cikin jam'iyyar APCn yace, lamarin abin ban takaici ne, inda yayi amfani da damar wajen kira ga manyan ƴan siyasa dasu tsawatarwa da mabiyan su domin gudun faruwar irin haka anan gaba.

To sai dai kuma, hukumar yan sanda ta jihar Zamfara har yanzu basu ce uffan akan lamarin ba, yayin haɗa wannan rahoton.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohi 28 da akayi zaɓe a Najeriya ranar asabar ɗin data gabata.

Zaɓen daya samu tasgaro na rigime rigime, kwacen akwatu, da kuma yin amfani da ƴan jagaliya domin haddasa rikici.

Kotu Tayi Hukunci Kan Babban Sanatan Najeriya a Ingila

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamnoni 28, Ta Ɗauki Mataki Kan Jihohi 2

Wata kotun sauraren ƙorafe korafen a Ingila ta kama tsohon shugaban majalisar dattawa ta Najeriya da laifin safarar sassan jikin dan adam a injila.

Wata kotun ƙasar Ingila ta samu tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da laifin safarar sassan jiki.

Bugu da ƙari, bayan kama Ike Ekweremadu da wannan laifin, kotun ta samu matar sa Beatrice, ƴar sa Sonia da likitan su Obinna Obeta, da laifi.

Masu yanke hukunci sun gano cewa su ukun sun haɗa baki ne domin kawo mai matashin zuwa birnin Landan, su yi amfani da ƙodar sa.

Wannan hukuncin dai shine na farko irin sa wanda aka taɓa zartarwa a ƙarƙashin dokar hana bauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar