A Yau INEC Za Ta Ci Gaba da Tattara Sakamakon Zabe a Jihohin Abia da Enugu
- Hukumar zabe ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihohi Abia da Enugu a yankin Kudancin Najeriya
- An dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna a wasu kananan hukumomin jihohin ne saboda samun matsala da aka yi
- Rikicin siyasa a jihar Taraba ya kai ga mutuwar wasu jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki a lokacin da ake tattara sakamakon zabe
Najeriya - Hukumar zabe zaman kanta (INEC) ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a kananan hukumomi uku na jihohin Enugu da Abia a yau Laraba 22 ga watan Maris.
Hukumar zaben ta dage ci gaba da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Obingwa ta Abia da kuma Nsukka da Nkanu East a jihar Enugu, TheCable ta ruwaito.
Festus Okoye, kwamishinan yada labarai na INEC ne ya sanar da batun ci gaba da tattara sakamakon zaben a ranar Laraba da rana a cikin wata sanarwa.
Bayanai daga hukumar zabe ta INEC
A cewar sanarwar:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Hukumar ta gama nazarinta. Don haka, za a ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohin Abia da Enugu a yau 22 ga watan Maris 2023.
“Hukumar ta yaba da hakuri da fahimtar da mutane suka yi a jihohin biyu har muka gama da tattara dukkan abubuwan da ake bukata.”
Yadda ala dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna
A baya an dage ci gaba da tattara sakamakon zaben ne biyo bayan suka da ake yiwa INEC daga bangaren ‘yan takarar gwamna a jam’iyyu daban-daban, rahoton The Nation.
Jam’iyyar PDP a jihar Enugu ta zargi hukumar zabe da saba ka’ida, inda tace hukumar ba ta da hurumin dakatar da tattara sakamakon zaben da aka riga aka kammala.
Zaben 2023 na gwamnoni a Najeriya ya zo da tsaiko da cece-kuce, lamarin da yasa a wasu jihohin aka yi tashin-tashina da rikici bayan siyasa.
An hallaka ‘yan sanda a wurin tattara sakamakon zabe
A wani labarin, kun ji yadda aka hallaka wasu jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki a ofishin hukumar zabe da ke jihar Taraba.
An ruwaito cewa, wasu sojoji ne suka hallaka jami’an tare da jikkata wasu biyu bayan barkwar rikici a tsakaninsu.
Ya zuwa yanzu, an sanar da sakamakon zaben wasu jihohi, wasu kuma ana ci gaba da kai ruwa rana kan sahihancin zaben.
Asali: Legit.ng