Dan Takarar Gwamnan NNPP a Taraba Ya Ce Shi Ya Lashe Zabe ba PDP Ba, Zai Antaya Kotu

Dan Takarar Gwamnan NNPP a Taraba Ya Ce Shi Ya Lashe Zabe ba PDP Ba, Zai Antaya Kotu

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sha caccaka a jihar Taraba bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar
  • Hukumar zaben ta alanta Kefas Agbu, dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri’u 257,926
  • A bangare guda, wanda ya zo na biyu a zaben, Sani Yahaya na NNPP ya ce ba zai amince da wannan sakamakon ba, zai tafi kotu

Jihar Taraba - Rikici ya biyo bayan zaben gwamnoni na 2023 a Najeriya, inda ake zargin aukuwar tashin hankali, murdiya da aringizon kuri’u a zaben da dai sauran matsaloli.

A jihar Taraba, dan takarar gwamna na NNPP, Sani Yahaya ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar.

A cewarsa, bai amince Kefas Agbu na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben, don haka zai maka Kefas, PDP da INEC a kotu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Zanga-Zanga Ke Gudana a Ofishin INEC Kan Ayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Wata Jiha

Sani Yahaya ya ce zai tafi kotu don kwace masa hakkinsa
Sani Yahaya, dan takarar gwamnan NNPP a jihar Taraba | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Dalilin da yasa Sani Yahaya zai kai kara kotu

Kamar yadda jarida TheCable ta ruwaito a ranar Talata 21 ga watan Maris, Sani Yahaya ya ce akwai alamomin tambaya da yawa game da zaben, don haka zai zarce kotu kawai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Muna da yakinin cewa wannan nasarar tamu ce. Za mu kalubalanci sakamakon ta kowacce hanya ta doka sannan mu tabbatar da nasararmu.
“Nasararmu tana nan a zahiri kuma za mu karbe ta. Ina kira ga jama’ar Taraba da su yi hakuri. Za mu kalubalanci sakamakon zaben saboda ni ne sahihin zababben gwamnan jihar Taraba.
“Ba za a tauye mana hakkinmu ba. Mun fara duba lamarin kuma muna kai.”

Kefas ne ya lashe zabe, inji hukumar zabe ta INEC

A tun farko kun ji cewa, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Kefas Agbu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da kuri’u 257,926, rahoton Daily Sun.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamna Na NNPP A Taraba Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe, Ya Bayyana Matakinsa Na Gaba

Sani Yahaya ne ya zo na biyu, inda ya samu kuri’u 202,277 a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP, kamar yadda INEC ta tattara.

Daga nan ne Yahaya yace ba zata sabu ba, kawai an yi murdiya ne, shi ne ya samu kuri’u mafi yawa a zaben.

NNPP ta karbi mulki a jihar Kano, Abba Gida-gida ya magantu

A wani labarin, kunji yadda jihar Kano ta samu sabon gwamna dan jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, na hannun daman Kwankwaso.

Bayan lashe zaben, Abba ya ce zai yi mulki ne daidai da muradin Kanawa, kuma zai bi tafarkin Kwankwaso sau da kafa.

Hakazalika, ya ce zai samar da ilimi kyauta ga al’ummar Kanawa, kana ya habaka kasuwanci da dai sauran lamura maso dadi ga ‘yan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.