'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Hedikwatar Jam'iyyar APC a Jihar Kano

'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Hedikwatar Jam'iyyar APC a Jihar Kano

  • Ɓata garin ƴan daban siyasa sun kai hari kan hedikwatar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano
  • Ƴan daban sun yi ƙone-ƙone a wurare daban-daban a jihar bayan an sanar da Abba Kabir Yusuf matsayin sabon gwamnan jihar
  • Ƴan daban sun kuma farmaki gidan shahararren mawaƙin nan Dauda Kahutu Rarara a yayin harin na su

Jihar Kano- Ƴan daban siyasa da dama masu murnar nasarar lashe zaɓen jam'iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) a zaɓen gwamnan da aka kammala sun farmaki hedikwatar jam'iyyar APC a jihar.

Ƴan daban sun kai hari ne kan hedikwatar jam'iyyar wacce ke kan titin hanyar Maiduguri a cikin birnin Kano bayan an sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Rahoton The Guardian

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Cafke Wani Dan Majalisa Da Sauran Masu Tayar Da Rikici a Jihar Kano

Ganduje
'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Hedikwatar Jam'iyyar APC a Jihar Kano Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Daga cikin abubuwan da aka lalata sun haɗa da motocin shahararren mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, waɗanda aka cinnawa wuta tare da gidan sa.

Wasu daga cikin matasan waɗanda suka mamaye kusan dukkanin titunan Kano, sun kuma ƙona gida da motoci a akan titin Zoo Road, waɗanda su ma mallakar mawaƙin ne. Rahoton Vanguard

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dama a jihar ana zaman ɗar-ɗar kan yiwuwar samun tashin hankali bayan bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Sai dai, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Muhammad Hussaini Gumel, yayi gargaɗi kan al'ummar jihar da su riƙa lura wajen yadda za suyi murnar lashe zaɓe.

Ya kuma buƙace su da suyi biyayya da dokar kullen da gwamnatin jihar Kano ta ƙaƙaba a jihar.

Yan Bindiga Sun Rike Wani Mutumin da Ya Kai N2m Na Fansar Matarsa Da ’Ya’yansa 3 da Aka Sace

Kara karanta wannan

Uba Sani Zai Gyara Kura-Kuran El-Rufai, Wasu Kungiyoyi a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun yi caraf da wani mutum da yaje kai maƙudan kuɗaɗen fansa wajen su.

Mutumin dai yaje ne kai kuɗin fansa domin a saku masa iyalan sa da ƴan bindigan suka sace a jihar Kaduna.

Mutumin dai yaje wajen ne ɗauke naira miliyan biyu na kuɗin fansar amma sai suka yi caraf suka riƙe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng