Sarkin Musulmi Ya Ce Musluman Najeriya Su Duba Jinjirin Watan Ramada Na a Ranar Laraba

Sarkin Musulmi Ya Ce Musluman Najeriya Su Duba Jinjirin Watan Ramada Na a Ranar Laraba

  • Sarkin Musulmi na Najeriya ya bukaci 'yan kasar da su fara duba jinjirin watan Ramadana daga ranar Laraba
  • Ya kuma bukaci 'yan kasar da su sanya ta a addu'o'insu na alheri a wannan watan mai alfarma
  • Hakazalika, ya nemi masu hannu da shuni da su tuna da 'yan uwansu Musulmai masu karamin karfi

Jihar Sokoto - Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) Sarkin Musulmi na Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci Musulman kasar da su fara duban jinjirin watan Ramadana da yammacin ranar Laraba.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da daraktan tafiyar da harkokin NSCIA, Arc. Zubairu Haruna Usman Ugwu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar sanarwar, an yanke shawarin hakan ne a wani zama da kwamitin duban wata na NMSC, inda shugaban kwamitin ya bukaci Musulmi su tuna cewa, ranar Laraba ce 29 ga watan Sha’aban na Hijira 1444.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya

A fara duba watan Ramadana
An yi kira ga fara duba jinjirin wata | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Alhamis ko Juma'a za a fara azumi

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa, ranar za ta yi daidai da 22 ga watan Maris na Miladiyyan Annabi Isah AS, kamar yadda ake lissafi dashi a Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar kwamitin, idan aka ga watan a ranar Laraba, za a tashi da Azumin watan Ramadana a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris 2023, kamar yadda ake sa ran Sarkin Musulmi zai sanar.

Idan ba a ga watan ba, Zubairu ya ce, ranar Juma’a 24 ga watan Maris ce za ta zama ranar 1 ga watan Ramadana a wannan shekarar.

Ku yiwa Najeriya addu’a a Ramadana

A bangare guda, kwamitin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su koma ga Allah tare da yiwa kasar addu’o’i masu amfani a watan mai alfarma, Premium Times ta tattaro.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci Sun ba Tinubu, Zababbun Shugabanni Shawara Kafin Shiga Ofis

A cewar kwamitin, ‘yan kasa ya kamata su dukufa da addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba ga kasar.

Hakazalika, an bukaci ‘yan kasa masu hannu da shuni da su taimakawa masu karamin karfi duba da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

A baya, sarkin ya sha bayyana matsayarsa game da matsin da ake ciki bayan sauyin fasalin Naira da aka yi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.