Tashin hankali A Taraba yayin da Ake ta Jin Karan harbe-harbe A Kusa da Ofishin INEC da Hedkwatar ‘Yan Sanda

Tashin hankali A Taraba yayin da Ake ta Jin Karan harbe-harbe A Kusa da Ofishin INEC da Hedkwatar ‘Yan Sanda

  • An samu tashin hankali a jihar Taraba yayin da ake ci gaba da aikin tattara sakamakon zaben gwamnan jihar
  • Rahoto ya bayyana cewa, an ji karan harbe-harbe daga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)
  • Hakazalika, an ce an ji harbi daga hedkwatar 'yan sandan jihar, lamarin da ya sa jama'a tserewa daga wuraren kasuwancinsu

Jihar Taraba - An samu rikici da tashin hankali a birnin Jalingo na jihar Taraba yayin da ake ta jin karan harbe-harbe a kusa ofishin INEC da hukuma hedkwatar 'yan sanda, Daily Trust ta ruwaito.

Ba a dai tabbatar da dalilin wadannan harbe-harbe ba, amma majiya ta bayyana zargin cewa, an samu sabani ne tsakanin jami'an tsaro da ke gadin ofishin na INEC.

An gaggauta garkame shaguna da harkokin kasuwanci, kana an ga tituna shuru yayin da iyaye ke kokari da gaggauta dauka 'ya'yansu daga makaranta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An sace ma'aikatan INEC 2 dauke da sakamakon zaben gwamnan wata jihar Arewa

Yadda rikici ya barke a Taraba, an ji karar harbe-harbe
Jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Usman Abdullahi bai amsa waya ba, kana bai dawo da sakon tes da majiya ta tura masa ba don jin halin da ake ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An dage zaben majalisa a wani yankin Kano

A jihar Kano, an samu tsaiko inda aka zargi yin aringizon kuri'u a wani yankin Takai da ke jihar a zaben 'yan majalisun wakilai.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce, inda hukumar zabe ta INEC tace bata amince da sakamakon da aka kawo daga yankin ba

A halin da ake ciki, hukumar ta ce dole za a sake zaben wasu rumfuna biyar na yankin don tabbatar da halin da ake ciki.

Ba wannan ne karon farko da ake samun tsaiko a zabukan jihar Kano ba, an yi hakan a zaben shugaban kasa da ya gudana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke a jihar Arewa, an harbe 'yan sanda 2 a hedkwatar INEC

An dakile masu kokarin kawo tsaiko ga zabe

A wani labarin, kun ji yadda jami'an sojin Najeriya suka yi maganin wasu 'yan ta'addan ISWAP da suka kai hari cibiyar tattara sakamakon zabe.

A cewar majiya, hakan ya faru ne jim kadan bayan da gwamnan jihar, Babagana Zulum ya kada kuri'arsa a mazabarsa.

An ruwaito cewa, akalla 'yan ta'adda 60 ne aka kashe nan take yayin da wasu suka tsere don gudun mutuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.