Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ayyana Zaben Wasu Mazabun Kano a Matsayin ‘Inconclusive’
- Rahoton da muke samu daga jihar Kano na bayyana yadda aka jinkirta bayyana sakamakon zaben majalisar wakilai
- Wannan ya faru ne sakamakon samun tsaiko a wasu rumfunan zaben mazabar Takai da jihar ta Arewa
- An kuma bayyana sakamakon zaben wasu mazabun jihar, inda da yawan APC suka lashe zaben na bana
Jihar Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Lahadi ta ayyana rashin amincewa da cikar sahihancin zaben mazabar Takai a majalisar jihar Kano.
Wannan na fitowa ne daga bakin baturen zaben Kano, Farfesa Usman Ibrahim a ofishin INEC da ke karamar hukumar Takai.
Rahoto ya bayyana yadda aka samu matsaloli a wurare daban-daban na kasar nan, ciki har da jihar Kano da ke Arewa maso Yamma, Legit.ng ta tattaro.
Dalilin da yasa aka dakatar da ayyana cikakken sakamakon zaben
A cewar baturen zabe:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Duk da cewa dan takarar APC, Musa Ali ya samu kuri'u 24,573 na NNPP kuma ya samu 23,569, ba mu da zabin da ya wuce mu ayyana rashin cikar sakamakon zaben.
"Wannan kuwa ya faru ne saboda an soke zaben rumfunan zabe biyar saboda wuce gona da iri na zaben.
"Yanzu, za a sake zaben a rumfunan zabe biyar."
Sakamakon zabe daga sauran mazabu
A bangare guda, hukumar zabe ta INEC ta ayyana Mr Garba Gwarmai na APC a matsayin dan zababben dan majalisar wakilai a mazabar Tsanyawa/Kuchi ta jihar Kano.
Baturen zabe, Farfesa Ganiyu Shokobi ne ya bayyana nasarar Mr Garba a cibiyar tattara sakamakon zabe na INEC da ke Tsanyawa.
A cewarsa, Gwarmai ya samu kuri'u 31,471 yayin da abokin hamayyarsa na NNPP, Mr Muhammad Ali ya samu kuri'u 27,864, dan takarar PDP kuwa ya samu kuri'u 136.
Sakamakon zaben majalisa daga Bagwai
Hakazalika, an sanar da sakamakon zaben mazabar Shanono/Bagwai, inda Ibrahim Kundila na APC ya fito a matsayin wanda ya yi nasara.
Kundila ya samu kuri'u 38,021 yayin da abokin hamayyarsa na NNPP, Musa Aliyu ya samu kuri'u 29,983 a zaben.
Baturen zabe, farfesa Ahmed Iliyasu ne ya sanar da sakamakon zaben, kamar yadda rahoto ya bayyana.
A baya kunji yadda 'yan daba suka farmaki gidan mawaki Dauda Kahutu Rarara a jihar ta Kano bayan zaben gwamna.
Asali: Legit.ng