Masu Zabe Sun Lakada Wa Wata Mata Duka Saboda Nuna Kuri'arta A Kano

Masu Zabe Sun Lakada Wa Wata Mata Duka Saboda Nuna Kuri'arta A Kano

  • An yi wa wasu mata duka saboda zargin satar kuri'a a rumfunan zabe daban-daban a jihar Kano
  • Rahotanni sun bayyana cewa wata mata mai suna Zubaida ta sha duka hannun mutane a Gundunar Giginyu
  • A wani rahoton a wani rumfar zabe a karamar hukumar Tarauni, masu zabe sun doki wata mata kan nuna kuri'arta a fili

Jihar Kano - A kalla mata uku ne aka lakada wa duka a rumfunan zabe daban-daban a jihar Kano kan zargin siyan kuri'u.

Wakilin Daily Trust a Gundumar Giginyu ya lura cewa an fitar da wata mata mai suna Zubaida daga rumfar zabe kan zargin siyan kuri'u yayin da ake zabe.

Masu kada kuri'a
An doki wasu mata kan zargin siyan kuri'a a Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Masu sayen kuri'u sun taru, sun lakadawa jami'an EFCC duka a jihar a Arewa

An kuma yi wa wata mata mai suna Amina duka kan zargin siyan kuri'un a rumfar zabe, amma an cigaba da zaben.

Masu zabe sun daki wata mata saboda nuna kuri'arta a Kano

Hakazalika, a rumfar zabe a karamar hukumar Tarauni, an yi wa wata matar duka saboda daga takardan zabenta bayan dangwale wa.

An rahoto cewa wasu wakilan jam'iyya sun nemi ta sayar musu da kuri'arta.

Amma, jim kadan bayan ta yi zaben, matar da daga takardan zabenta sama don tabbatar musu, hakan ya fusata wasu kuma suka far mata.

Jami'an tsaro sun yi gaggawa sun shiga tsakani suka kwantar da tarzomar sannan aka yi gaba da matar.

Muhimman abubuwa 10 dangane da Dr Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

A wani rahoto mai kama da wannan, Legit.ng ta kawo muku muhimman bayanai dangane da dan takarar gwamna na jihar Kano karkashin jam'iyyar APC, Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan

'Yunwa A Ƙasa': Masu Kaɗa Ƙuri'a Sun Ƙi Karɓar Tiransifa, Sun Buƙaci Abinci A Babban Jihar Arewa

Gawuna, gogaggen dan siyasa ne wanda ya yi aiki da gwamnatoci uku a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164