NJC Ta Kori Alkalin Alkalai Na Jihar Taraba, Ta Bayyana Dalili

NJC Ta Kori Alkalin Alkalai Na Jihar Taraba, Ta Bayyana Dalili

  • Majalisar Alkalan Najeriya, NJC, ta dakatar da Alkalin Alkalan Jihar Taraba, Mai Shari'a F.B. Andetur kuma ta umurci a masa ritayar dole
  • NJC ta dauki wannan matakin ne bayan bincike da ta yi ta gano Andetur ya yi wa doka karan tsaye ta hanyar jinkirta yanke hukunci tsawon wata 30 bayan an gama gabatar da shaidu da hujoji
  • Majalisar ta umurci Andetur ya mika mukaminsa ga Alkali mafi girma a jihar kafin a tabbatar da masa ritayar, sannan ta ce tana bincikar wasu alkalan

FCT, Abuja - Majalisar Alkalai Na Kasa, NJC, ta bada umurci Alkalin Alkalai, CJ, na Jihar Taraba, Mai Shari'a F.B. Andetur, ya bar ofishinsa nan take, rahoton Vanguard.

Majalisar, wacce ke karkashin jagorancin Alkalin Alkalai na Kasa, CJN, Mai Shari'a Kayode Ariwoola, ta umurci CJ din na Taraba ya mika mukami ga Alkali mafi girma a jihar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya

Alkalin Alkalan Jihar Taraba
NJC ta dakatar da Alkalin Alkalai na Jihar Taraba, ta umurci a masa ritaya na dole. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A sanarwar da ta raba wa manema labarai a ranar Juma'a a Abuja, NJC, ta ce a karshen taronta na ranar 16 ga watan Maris, ta yanke shawarar a yi wa CJ din ritaya na dole, sakamakon abin da ta gano yayin bincike kan korafi da aka shigar a kansa.

Dalilin korar Alkalin Alkalan Jihar Taraba, NJC

Ta ce CJ din na Taraba ya dakile hukunci ta hanyar jinkirta yanke hukunci kan kara mai lamba TRSJ/134/17: Mallam Kassim Yahaya Ahmad Vs Shittu Wurmo & Shuwari Farms Limited, wata 30 bayan bangarorin biyu sun gabatar da jawabansu na karshe.

NJC cikin sanarwa mai dauke da sa hannun Direktan watsa labarai, Mr Soji Oye ta ce:

"Majalisar, bayan tattaunawa ta samu Alkalin Alkalan da saba sashi na S.294(1) na kundin tarayyar Najeriya don haka ta bada shawarar yi masa ritaya na dole nan take a sanar da Gwamna Darius Dickson Ishaku na Jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci Sun ba Tinubu, Zababbun Shugabanni Shawara Kafin Shiga Ofis

"A yanzu, Majalisar ta yi amfani da ikon da doka ya bata a kundin tsarin mulki na 1999, da aka yi wa gyara, na dakatar da Mai shari'a Andetur har zuwa lokacin da za a masa ritayar na dole.
"Ya mika aiki ga Alkali mafi girman mukami a jihar."

An kafa kwamiti don bincikan wasu alkalan

Har wa yau, Majalisar ta ce ta kafa kwamiti don bincika korafi kan wasu alkalai, duk da cewa ba ta bayyana sunansu ba, ta ce suna cikin korafi bakwai da aka gabatar mata, amma ta yi watsi da uku.

Shari'ar Murja Kunya: An sake komawa kotu, Alkali ya umurci a cigaba da tsare ta a gidan gyaran hali

A wani rahoton kun ji cewa a ranar 16 ga watan Fabrairu, an sake gurfanar da fitacciyar yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya a kotun musulunci da ke Filin Hoki a Kano.

Kamar yadda Arewa Radio ta rahoto, Alkali ya umurci a mayar da Murja Kunya gidan kaso ta sake yin mako guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164