An Kashe Mutum 4 Yayin Arangama Tsakanin Yan Shi'a Da Tawagar El-Rufai A Kaduna

An Kashe Mutum 4 Yayin Arangama Tsakanin Yan Shi'a Da Tawagar El-Rufai A Kaduna

  • Ana fargabar rayyuka hudu sun salwanta a Kaduna yayin arangama tsakin yan Shi'a da tawagar Gwamna El-Rufai a unguwar Bakin Ruwa
  • Yayin da tawagar ke kokarin wucewa an jefe ta da duwatsu tare da ihu hakan ya janyo hatsaniya kuma jami'an tsaro suka yi harbi har hakan ya janyo rasa rai
  • Mai magana da yawun yan Shi'a a Kaduna, Abdullahi Usman, ya ce babu wanda aka kashe cikin mambansu kuma ya musanta cewa mambobinsu sun jefi tawagar gwamnan

Kaduna - Ana zargin an kashe mutane hudu yayin da jami'an tsaro da ke tare da tawagar Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna suka yi arangama da yan Shi'a a Bakin Ruwa na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar Alhamis.

Babu cikakken bayani dangane da faruwar abin a yanzu amma majiyoyi sun fada wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 4 na yamma yayin da gwamnan na ziyarci unguwar.

Kara karanta wannan

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

El-Rufai
Yan Shi'a sun yi arangama da tawagar Gwamna El-Rufai A Kaduna, ana fargabar mutum hudu sun mutu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

An tattaro cewa tawagar gwamnan sun hadu da yan Shi'an ne da ke win taronsu na mako-mako a Bakin Ruwa kan babban hanyar Nnamdi Azikwe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan uwan wani cikin wadanda aka kashe ya magantu

A cewar Tasiu Mohammed, wani ganau, wasu cikin yan Shi'an sun fara ihu yayin da tawagar gwamnan ke kokarin wucewa ta cikin masu taron.

Ya ce hakan ya janyo hatsaniya a yayin da jami'an tsaron suka bude wuta lokacin da wasu cikin matasan suka fara jifarsu da duwatsu.

Dan uwan Yushehu Mohammed, daya cikin wadanda suka rasu, ya ce dan uwansa da aka kashe ba dan Shi'a bane, direba ne da harsashi ta harba.

Ya ce:

"Abin bakin ciki ne. An kira mu an fada mana cewa an harbi dan uwan mu wanda ke aikin tuki da harsashi."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Soja, Wasu Sojoji 3 da Jami'an Tsaro a Jihar Arewa

Ya bukaci a yi bincike tare da biyansu diyya domin dan uwansa yana da aure.

Daily Trust ta tattaro cewa jami'an tsaron kuma sun kama wasu cikin matasan sun tafi da su.

Ba a kashe mamban mu ba, wakilin yan Shi'a na Kaduna

Da aka tuntube shi, wakilin yan Shi'a a Kaduna, Abdullahi Usman, ya ce babu mambansu cikin wadanda aka kashe.

A cewarsa, direbobin motoccin haya ne da ke kusa da wurin lodi inda abin ya faru.

Ya kuma ce ba gaskiya bane cewa mambobinsu sun jefi tawagar da duwatsu.

Kakakin yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce ana bincike kan lamarin kuma zai fitar da sanarwa daga baya.

Sunayen Yan Shi'a 6 Da Jami'an Tsaro Suka Harbe Har Lahira a Kaduna

A wani rahoton a baya, kun ji cewa a ranar 8 ga watan Agustan 2022, wasu mabiya Shi'a sun fito don tattakin muzaharar Ashura.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al’ummar Jihar Kano Ana Gab Da Zabe

Amma bisa tsautsayi, sunyi arangama da jami'an tsaro a garin Zariya a Kaduna inda wasu suka rasa rayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164