Najeriya Na Daga Cikin Kasashe 10 Da ’Yan Kasar Ba Sa Iya Neman Rancen Kudi Su Samu

Najeriya Na Daga Cikin Kasashe 10 Da ’Yan Kasar Ba Sa Iya Neman Rancen Kudi Su Samu

 • Najeriya, Laberiya, Ghana da Zimbabwe da wasu kasashen Afrika shida ne kasashen da suka fi kowacce kasa kudin ruwa mafi yawa a nahiyar
 • Mai bincike ya bayyana cewa, yawan kudin ruwa na rage yawan kashe kudin jama’a, hakan nan yana rage samun dama ga ‘yan kasa su karbi rance
 • Hakazalika, masanin ya ce, yawan kudin ruwan na hana kasa damar fitar kayayyakinta zuwa wasu kasashe, kuma hakan na karya darajar kudi

Afrika - A cewar babban bankin Najeriya (CBN), kaso 17.5% ne kudin ruwa ga rance a Najeriya, dalili kuwa, hauhawar farashin kayayyaki ya lakume kudaden da aka ajiye, wanda ya kai akalla 22% a Najeriya a yanzu.

Illar yawan kudin ruwa ga kasa na da yawa, amma mafi munin hakan shine, yana lakume kudaden shiga tare da sanya kunci ga ‘yan kasa, musamman wajen neman rance, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya, zai shafi Najeriya

Yawan kudin ruwa na sanya ‘yan kasa su rasa damar cin bashin banki, wanda ke rage yawaitar siyan kayayyaki, daga karshe hakan kuma ya rage siyayya daga gama-garin mutane, kankat kuma ya shafi tattalin arzikin kasa.

Najeriya na cikin kasashen da rancen kudi ke ba da wahala
Kudaden Najeriya, sabbi da aka sauya | Hoto: The Yudel Media
Asali: Getty Images

Yawan kudin ruwa na kassara kasuwanci

Hakazalika, yawan kudin ruwa na iya kassara kasuwanci a kasa tare da koran masu zuwa hannun jari, wanda hakan zai shafi kasar baki daya, sannan ya karya darajar kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bangare guda, fitar da kayan haja zuwa kasashen waje ka iya zama matsala, domin dole zai rage yadda jama’a ke fitar da kayayyaki waje duk dai ta sanadiyyar yawan kudin ruwa.

Amma duk da haka, yawan kudin ruwa na sanya yawan ajiye kudi a banki tare da rage kashe-kashen kudi a tsakanin jama’a saboda mutane za su rike kudade don kuwa tsadar kayayyaki zai karu, wanda ka iya rage yaduwar kudade.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 Bayan Rasa Rayyuka 17, Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari

Zimbabwe ta fi yawan kudin ruwa a kasashen Afrika

 1. Zimbabwe: 150%
 2. Ghana: 28%
 3. Sudan: 27.3%
 4. Sierra Leone: 18.25%
 5. Malawi: 18%
 6. Angola: 18%
 7. Nigeria: 17.5%
 8. Mozambique: 17.25%
 9. Egypt: 16.25%
 10. Liberia: 15%

Farashin danyen mai ya fadi a duniya

A wani labarin kuma, kun ji yadda farashin mai ya fadi a duniya, inda ya sauka zuwa $72, karo na farko kenan tun Disamban shekarar 2021.

Wannan lamarin ya shafi Najeriya kai tsaye, inda hakan zai shafi abubuwa da dama ciki har da kasafin kudin da gwamnati ta yi.

Ba Najeriya kadai ba, kasar Amurka na daga cikin kasashen da hakan ya shafa, inda farashin danyen man kasar shi ma ya sauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel